logo

HAUSA

Amurka Mai Son Leken Asirin Sauran Kasashe Ba Ta Da Amana

2021-06-01 19:54:00 CRI

Amurka Mai Son Leken Asirin Sauran Kasashe Ba Ta Da Amana_fororder_微信图片_20210601195337

Kwanan baya, gidan rediyon Denmark ya gabatar da wani shiri na musamman, inda ya fayyace yadda hukumar tsaron kasar Amurka take yiwa Denmark leken asiri ta hanyar amfani da Intanet din kasar bisa taimakon hukumar leken asirin kasar, don sa ido kan shugabannin kasashen Turai da dama ciki hadda shugabar gwamnatin Jamus Angela Dorothea Merkel.

Amurka ta sake nuna fuska biyu kan batun tsaron kasa, inda take kiran kanta da “Mai tabbatar da tsaron Intanet” ta zama mai leken asiri mafi girma a duniya, tare da sa ido kan kawayenta.

Amurka ta dade tana yiwa kasashen Turai leken asiri, tun daga shekarar 2013, tsohon ma’aikacin mai kwarmata bayanai, Edward Snowden ya fayyace yadda Amurka take sauraron wayoyin shugabannin kasashen ketare, ya ce, an saurari bayanan wayar Angela Dorothea Merkel har tsawo shekaru 10. Abin da ke faruwa a kwanakin baya-baya nan na nuna cewa, Amurka ba ta dakatar da aikinta a Turai ba.

Manazarcin huldar kasa da kasa na kasar Birtaniya Tom Fowdy ya ce, Washington hakikanin babbar barazana ce ga Turai. Kasashen Turai da dama ciki hadda Jamus, Faransa, Norway da Sweden da sauransu sun hada kansu don nun rashin jin dadi kan lamarin. Amma, Amurka ba ta ba da amsa har wa yau ba tukuna.

Nan da kwanaki 10, shugaban kasar Amurka Biden zai kai ziyara nahiyar Turai, ziyarar ta farko tun bayan da ya hau kujerar shugabancin kasar. Duk da karairayin da wasu ‘yan siyasar Amurka suke yi, Amurka ba ta da amana ko kadan a duniya. Kamata ya yi Turai ta fahimci halin da ake ciki game da huldar Amurka da Turai, ta farka daga mafarkin kyautata huldarsu mai kyau. (Amina Xu)