logo

HAUSA

Babban kamfanin fasahar Sin Huawei ya fadada ayyukan fasahar 4G zuwa arewacin Habasha

2021-06-01 10:46:58 CRI

Babban kamfanin fasahar Sin Huawei ya fadada ayyukan fasahar 4G zuwa arewacin Habasha_fororder_0601-Huawei-Ahmad

Katafaren kamfanin fasahar nan na kasar Sin Huawei, ya sanar da cewa, ya fadada ayyukan samar da fasahar sadarwa ta 4G zuwa birane shida na arewa maso gabashin kasar Habasha.

Da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, Zhang Bowen, mataimakin daraktan hulda da jama’a na kamfanin Huawei shiyyar arewacin Afrika, ya ce, kamfanin Huawei ya yi hadin gwiwa da kamfanin sadarwa mallakin gwamnatin kasar Habasha wato Ethio-Telecom wajen kaddamar da fasahar sadarwan ta 4G zuwa biranen kasar a ranar Lahadi.

Biranen su ne Dessie, Kemise, Kombolcha, Kemise, Woldiya da Lalibela.

Bugu da kari, kamfanin Huawei ya shirya kaddamar da ayyukan fasahar ta 4G a yankuna jahar Afar dake shiyyar arewa maso gabashin kasar Habasha a wata mai zuwa, a cewar Zhang.

Zhang ya kara da cewa, a watanni ukun da suka gabata kamfanin Huawei ya taimaka wajen fadada ayyukan fasahar sadarwa ta 4G a kudu maso gabashin kasar da kuma arewa maso yammacin kasar ta Habasha.

Kafin wannan lokaci, Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha shi kadai ne yake amfani da fasahar sadarwa ta 4G a kasar. (Ahmad Fagam)