logo

HAUSA

Xi: Abu mafi muhimmanci shi ne yara su girma lami lafiya

2021-06-01 11:09:21 CRI

Idan yara sun girma lami lafiya, hakan zai baiwa kasar da suke rayuwa cikin ta damar ci gaba yadda ya kamata. A don haka babban sakataren JKS Xi Jinping, yake mai da hankali matuka kan yara a ko da yaushe. Haka kuma yana kula da harkokinsu na yau da kullum, kamar abinci, da tufafi, da lafiyar jiki, da samun ilmi a makarantu, da kuma samun horo a wajen makaranta.

A ranar yara ta duniya, wato ranar 1 ga watan Yuni, bari mu waiwayi soyayyar da Xi yake nunawa yara..

Xi: Abu mafi muhimmanci shi ne yara su girma lami lafiya_fororder_2020年9月习近平来到文明瑶族乡第一片小学看望学生

A ranar 16 ga watan Satumban shekarar 2020, daliban makarantar firamare dake garin Wenming ta kabilar Yao, na gundumar Rucheng ta lardin Hunan dake kudancin kasar Sin, sun ga kaka Xi da idonsu, inda babban sakataren JKS Xi Jinping, wanda ke yin rangadin aiki a lardin ya shiga ajinsu, domin koyon darasin siyasa tare da su. A cikin ajin, Xi ya waiwayi labaran da suka faru a kan hanyar doguwar tafiya, da jajayen dakarun sojin kasar suka yi kafin shekaru sama da 80 da suka gabata, inda ya bayyana cewa,“Ina farin ciki matuka, saboda na ga kuna koyon labaran dake shafar jarumai da suka shiga doguwar tafiya. Za mu ciyar da babban sha’aninmu na juyin juya hali, da hanyarmu ta raya kasa gaba, daga zuriya zuwa zuriya. Ina fatan za ku cimma babban burinmu na farfado da al’ummun Sinawa.”

A ranar yara ta shekarar 2018, Xi ya taba amsa wasikar da daliban makarantar firamare ta jajayen dakarun soji ta kauyen Beiliang na garin Zhaojin dake birnin Tongchuan na lardin Shaanxi na kasar suka aika masa, inda ya kara karfafa zukatan su da cewa, ya dace yara su kara fahimtar ilmomin tarahin dake shafar juyin juya hali, da gine-gine da kwaskwarima na kasar Sin. Haka kuma, ya dace su yi koyi da jarumai masu ba da misali, domin kara kishin JKS, da kasar Sin, da kuma al’ummun kasar, ta yadda za su ciyar da halin juyin juya hali gaba, ta hanyar daukar hakikanin matakai. A cewarsa:“Bai kamata a yi tsimin kudi a fannin ba da ilmi ga yara ba. Ya dace a mai da hankali kan girmansu tun suna kanana. Ta haka ne kowane yaro zai samu damar nuna rinjayensa a zaman rayuwarsa na yau da kullum.”

A farkon bana, kasar Sin ta sanar da cewa, ta samu cikakkiyar nasarar kawar da talauci a fadin kasar daga duk fannoni. Hakika a cikin shekaru 8 da suka gabata, wato yayin da ake kokarin kawar da talauci a kasar, jam’iyyar kasar Sin, da gwamnatin kasar suna ba da muhimmanci matuka ga aikin ba da ilmi ga yara a yankunan dake fama da talauci. Sau da yawa Xi Jinping ya yi nuni da cewa, dole ne a samar da damar samun ilmi ga yara dake rayuwa a yankunan dake fama da talauci, kuma ya kan shiga makaranta yayin da yake rangadin aiki a fadin kasar, domin kara fahimtar yanayin karatu da zaman rayuwa da yara suke ciki.

Xi: Abu mafi muhimmanci shi ne yara su girma lami lafiya_fororder_2019年4月习近平来到重庆石柱土家族自治县中益乡小学考察

Misali a makarantar firamare ta garin Zhongyi na gundumar Shizhu ta birnin Chongqing, Xi ya duba dakin cin abincin makarantar a tsanake, inda ya bayyana cewa,“Wadannan yara na da matukar daraja ga iyalansu. A don haka dole ne ku kula da su yadda ya kamata a nan, saboda ba ma kawai ku malamansu ba ne, har ma ku ne iyayensu na wucin gadi. Aikinku yana da muhimmanci, ya zama wajibi ku tabbatar da tsaron yara, da kuma tsaron abinci.”

A makarantar firamaren sabon kauye, Xi ya yi farin ciki kwarai da ya ga an shirya kwas din koyar da wasan kwallon kafa, da wasan kwallon kwando, da wasan kwallon tebur, ya kuma kara karfafa zukatan yaran dake wasan kwallon kafa da cewa, ya dace su kara motsa jiki, ta yadda za su daga matsayin wasan na kasar Sin.

Lafiyar jiki da hankali ta yara, tana shafar makomar kasa da al’ummun kasar. Shi ya sa a yayin taruka biyu na bama, Xi Jinping ya tunatar da cewa, ya dace a kara mai da hankali kan lafiyar hankalin yara, kuma bai kamata a mai da hankali kan makin jarrabawar darasi kadai ba, yana mai cewa,“Aikin ba da ilmi, ko a cikin makaranta, ko a gida, bai kamata ya tsaya ga makin jarrawaba kadai ba. Babu nasara idan yara ba su girma yadda ya kamata ba, wato ba su girma da hali na gari ba.”

Xi: Abu mafi muhimmanci shi ne yara su girma lami lafiya_fororder_2019年4月习近平和少先队员一起参加首都义务植树活动

Haka zalika, tun daga shekarar 2013, Xi Jinping ya dinga halartar aikin shukan itatuwa da aka shirya a nan birnin Beijing tare da yara, inda ya kan gaya musu cewa, ya dace su kara motsa jiki, ta yadda za su girma lami lafiya kamar yadda kananan itatuwa suke, yana mai cewa,“Ina fatan yaran kasar Sin, za ku kara karfafa motsa jikinku a waje, ko bayan karatu. Misali ku kara shuka itatuwa, ina fatan za ku girma lami lafiya kamar kananan itatuwa.”(Jamila)