Kafofin yada labaru na Denmark: NSA na Amurka ta hada kai da hukumar leken asiri ta tsaron Denmark wajen sa ido kan shugabannin wasu kawayensu
2021-05-31 13:58:41 CRI
Ranar 30 ga wata, kamfanin dillancin labaru na kasar Denmark ya gabatar da shirin musamman, inda a cewarsa, hukumar kula da harkokin tsaron kasar Amurka wato NSA, ta samu iznin hukumar leken asiri ta tsaron Denmark, domin shiga yanar gizo ta Denmark, inda take tara bayanan asali, ta yadda za ta sa ido kan shugabannin wasu kasashe. Alal misali, akwai shugabar gwamnatin kasar Jamus, da shugabannin kasashen Faransa, da Sweden, da Norway da wasu manyan ‘yan siyasan kawayensu da ake kokarin sa ido a kansu.
An ruwaito cewa, bisa bayanai daga wata majiyar hukumar leken asiri da tsaron Denmark, kamfanin dillancin labaru na Denmark ya hada kai da kafofin yada labaru na Sweden, da Norway, da Jamus da Faransa, wajen gano hakan daga wani binciken da aka gudanar a asirce, kan hukumar leken asiri ta tsaron Denmark.
To sai dai kuma, an ce ministar tsaron Denmark Trine Bramsen ta amsa wata wasikar Email daga kamfanin dillancin labaru na Denmark da yammacin wannan rana, inda ta ce, ba ta yarda da a sa ido a asirce kan kawayen Denmark ba. Haka kuma gwamnatin Norway da Sweden sun bukaci gwamnatin Denmark ta ba da amsa kan wannan zargi nan take. (Tasallah Yuan)