logo

HAUSA

Amurka Ta Sake Yada Jita-Jitar Bullar Kwayar Cuta Daga Dakin Gwaji Domin Cimma Mummunan Burinta Na Siyasa

2021-05-31 21:29:36 CRI

Amurka Ta Sake Yada Jita-Jitar Bullar Kwayar Cuta Daga Dakin Gwaji Domin Cimma Mummunan Burinta Na Siyasa_fororder_210531-bayani-maryam2-hoto

Michael Ryan, darekta mai kula da shirin gaggawa na hukumar kiwon lafiyar duniya ta WHO, ya bayyana cewa, yanzu wasu na kokarin kawo cikas ga aikin binciken gano asalin kwayar cutar numfashi ta COVID-19 bisa wasu matakan siyasa.

Ya yi wannan tsakoci ne a kwanan baya, domin zargin kasar Amurka kan yadda take yada jita-jita cewar, wai kwayar cutar numfashi ta COVID-19, ta bulla ne daga dakin gwaji.

Wasu masana kimiyya na ganin cewa, kasar Amurka na yada wannan labarin karya ne, domin cimma mummunan burinta na siyasa, sabo da, an riga an musanta wannan labari bisa nazarin da aka yi a baya. Yanzu haka ma, hukumar leken asiri ta kasar Amurka ta fidda sanarwa, inda ta nuna amincewarta kan ra’ayi daya da aka cimma, wato kwayar cutar COVID-19 ba mutane ba ne suka kirkire ta

An fidda wannan ra’ayi ne a watan Maris na bana, bayan ziyarar aiki da tawagar masanan hukumar WHO ta sha kawowa kasar Sin, kuma bisa binciken kimiyya da hukumar ta yi, ta sanar da cewa, ba zai yiwu kwayar cutar COVID-19 ta bulla daga dakin gwaji ba.

Amma, abin bakin ciki shi ne, wasu ‘yan siyasar kasar Amurka suna ci gaba da yada jita-jita, domin bata sunan kasar Sin, ko da abin ya saba da matakai na kimiyya.

Kamar yadda kasar Amurka ta yada jita-jita cewar, wai kasar Iraq ta mallaki makamai masu guba, yanzu, ta fara zargin dakin gwajin birnin Wuhan, lamarin da ya nuna mana mugun burin na kasar Amurka a fannin siyasa.

Aikin binciken gano asalin kwayar cutar numfashi ta COVID-19, aiki ne na masana kimiyya, ba aiki ne na masu leken sirri na kasar Amurka ba. Cikin shekara daya ko fiye, masanan kasa da kasa ba su cimma nasarar ganon asalin kwayar cutar ba, amma, abin dariya shi ne, kasar Amurka ta ce, masu aikin leken sirri na kasar sun yi nasarar gano asalin kwayar cutar cikin kwanaki 90. Tabbas, ba wanda zai yarda da ita.

Bugu da kari, kwararren hukumar WHO Dominic Dwyer ya bayyana cewa, babu shaidun da suka nuna cewa, kwayar cutar ta bulla ne daga dakin gwaji, kuma, kasar Sin tana goyon bayan hukumar kan aikin binciken gano asalin kwayar cutar yadda ya kamata. Cikin babban taron kiwon lafiyar duniya karo na 74, wakilan wasu kasashe sun kuma nuna yabo matuka ga kasar Sin, dangane da yadda ta yi bayani game da kwayar cutar COVID-19 ga kasa da kasa cikin sauri, da kuma babbar gudummawar da ta baiwa kasa da kasa a fannin samun alluran rigakafi, matakan da suka taimakawa kasashen duniya wajen yaki da annobar cutar COVID-19. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)