logo

HAUSA

Wace rawa Sin ke takawa ga ayyukan MDD don warware rikicin kasa da kasa?

2021-05-31 15:51:43 CRI

Wace rawa Sin ke takawa ga ayyukan MDD don warware rikicin kasa da kasa?_fororder_A

Masu hikimar magana na cewa, “yabon gwani ya zama dole.” Daya daga cikin manyan dabarun salon harkokin diflomasiyyar da kasar Sin ta fi amfani da su shi ne kokarinta wajen yin kiraye-kiraye ga dukkan bangarorin kasa da kasa da su rungumi amfani da salon warware duk wata takaddama ko jayayya ta hanyar lalama wato ma’ana a bi komai a sannu-sannu ta hanyar tattaunawar siyasa domin cimma maslaha a maimakon yin amfani da karfin tuwo ko kuma bakin bindiga wanda a mafi yawan lokuta babu abin da hakan ke haifarwa face kara dagula al’amurra. Ko shakka babu, kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da warware sabani ko rashin fahimta a tsakanin bangarorin da ba sa ga maciji da juna a matakai daban daban na kasa da kasa. Alal misali, koda a karshen makon da ya gabata, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya bukaci kwamitin sulhun MDD ya dauki kwararan matakan da za su tabbatar da warware rikici tsakanin al’ummar Falasdinu da Isra’ila.

Jakadan na Sin ya ce babban nauyin dake kan kwamitin sulhun MDD shi ne kiyaye tsaro da zaman lafiyar kasa da kasa, don haka, tilas ne kwamitin ya dauki kwararan matakan daidaita rikicin Falastinu da Isra’ila. A cewar jami’in diflomasiyyar na Sin, rikicin da ya barke na baya bayan nan ya sake tunatar da duniya cewa, bai kamata a zura ido ana kallon al’amurran dake shafar yankin gabas ta tsakiya suna ci gaba da tabarbarewa ba, ko kuma a ci gaba da kaiwa al’ummar Falastinawa bango, ko mantawa da sauran batutuwan dake shafar kudurorin da kwamitin sulhun MDDr ya amince da su, ko kuma yin watsi da hakikanin nauyin dake bisa wuyan kwamitin sulhun MDD wadanda suka zama wajibi ya sauke su. Ga dukkan masu bibiyar yadda al’amurran kasar Sin ke wakana, za a iya fahimtar yadda mahukuntan kasar ke kara jaddada aniyar gwamnatin kwaminis wajen daidaita al’amurra cikin ruwan sanyi a maimakon tada jijiyar wuya, ko yin shagube, ko haifar da tunziri. Yadda kasar Sin ke nuna goyon baya gami da tinkarar al’amurran dake shafar zaman lafiyar kasa da kasa ba wani boyayyen al’amari ba ne, ko da a karshen wannan makon jakadan na Sin a MDD ya jinjinawa dakarun wanzar da zaman lafiyar MDD bisa muhimmiyar rawar da suke takawa wajen tabbatar da tsaro da dorewar zaman lafiyar duniya kana ya jaddada aniyar kasar Sin na tallafawa shirin wanzar da zaman lafiyar MDD.

A sakonsa na tunawa da ranar zaman lafiya ta kasa da kasa, wacce ta fado a ranar 29 ga watan Mayu, Zhang, ya gabatar da sakon girmamawa da nuna yabo ga dukkan dakarun ayyukan wanzar da zaman lafiya dake sassa daban daban na duniya. Ya gabatar da jinjina ga dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD sama da 4,000 wadanda suka sadaukar da rayuwarsu domin tabbatar da zaman lafiyar duniya. Zhang Jun ya ce, hanya mafi dacewa ta nuna girmamawa ga jaruman da suka rasa rayukansu a bakin aiki shi ne a tabbatar da dorewar ayyukan wanzar da zaman lafiya. A cewarsa kasar Sin ta kasance kasa ta biyu mafi girma a duniya dake bayar da gudunmawa ga ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD wajen bayar da taimakon kudade a kan lokaci, kana kasar Sin ita ce kasar dake sahun gaba a duniya wajen bayar da gudunmawar dakarun sojoji da na ’yan sanda a cikin kasashen mambobin kwamitin sulhun MDD biyar masu wakilcin dindindin a kwamitin sulhun. Yayin da dakarun kiyaye zaman lafiyar ke kokarin baiwa duniya kariya, kasar Sin a shirye take ta ci gaba da ba su kariya, in ji mista Zhang. A shekarar da ta gabata, karkashin shirin da kasar Sin ta bullo da shi, kwamitin sulhun MDDr ya amince da kudiri mai lamba 2518, kudiri na farko ya shafi batu ne na kiyaye tsaron lafiyar dakarun wanzar da zaman lafiya. A watan da ya gabata, kasar Sin, tare da wasu kasashen duniya, sun kafa wata kungiyar abokai mai rajin tabbatar da tsaron lafiyar dakarun wanzar da zaman lafiya. A makon da ya gabatan kuma, kasar Sin ta jagoranci bude taron mahawarar kwamitin sulhun MDD mai dauke da wannan taken. Ko shakka babu, Sin ta cira tuta wajen tabbatar da zaman lafiyar kasa da kasa. (Ahmad Fagam)