logo

HAUSA

Sharhi:Yadda kasar Sin take ciyar da al’ummarta biliyan 1.4

2021-05-31 21:24:24 CRI

 

Sharhi:Yadda kasar Sin take ciyar da al’ummarta biliyan 1.4_fororder_微信图片_20210531211829

A nan kasar Sin, watan Mayu lokaci ne da amfanin gona suka fara nuna kuma aka fara girbi na lokacin damina. Rahotanni daga ma’aikatar kula da harkokin ayyukan gona da kauyuka ta kasar Sin na cewa, ya zuwa ranar 29 ga wata, yawan alkama da aka girbe ya kai kadada miliyan 13.35, kuma ana sa ran samun girbi mai armashi. Girbin da ake yi a lokacin damina shi ne na farko da a kan yi a shekara a kasar, kuma sama da kaso 90% na amfanin gona da aka girbe a lokacin alkama ne, wanda ke da matukar muhimmanci ga aikin samar da abinci a kasar.

Abinci shi ne tushen rayuwar dan Adam, kuma batun tsaron abinci na shafar zaman lafiya da kwanciyar hankalin duniya. Sai dai har yanzu shi ne kalubalen da dimbin kasashe masu tasowa suke fuskanta. Kasancewar kasar Sin ita ce kasa ce mafi yawan al’umma a duniya, yadda take iya ciyar da al’ummarta biliyan 1.4 na da muhimmiyar ma’ana ga samar da kwanciyar hankali da ci gaba a kasar. Duk da haka, ba aiki ne mai sauki ba, musamman ga kasar da take da al’umma sama da biliyan 1.4 wadda kuma ke da filayen gona da fadinsu ya kai kadada miliyan 130 kawai, wato ma’ana tana da nauyin ciyar da kaso 20% na al’ummar duniya amma da kaso 9% na filayen gona na duniya baki daya.

Sinawa masu dogon shekaru, ba za su manta da yunwar da suka taba fuskanta ba. A yayin da aka kafa jamhuriyar jama’ar kasar a shekarar 1949, yawan hatsin da aka samar a kasar ya kai kimanin ton miliyan 110, wato ke nan yawan hatsin da kowane dan kasar ya mallaka kilogiram 209 ne kawai. A lokacin, wasu sun yi hasashen cewa, jam’iyyar kwaminis ta kasar ba za ta iya daidaita matsalar abinci ga al’ummar kasar ba, sabo da “babu wata gwamnati da ta kai ga daidaita wannan matsala a kasar”. Amma ga shi a karkashin jagorancin jam’iyyar kwaminis ta kasar, batun karancin abinci ya zama tarihi. To, shin yaya jam’iyyar kwaminis da ke mulkin kasar ta kai ga ciyar da al’ummar kasar biliyan 1.4 kuma?

Sharhi:Yadda kasar Sin take ciyar da al’ummarta biliyan 1.4

Na farko, bayan kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin, jam’iyyar kwaminis mai mulkin kasar a kullum tana mai da batun ciyar da al’ummar kasar a matsayin babban aiki na farko da ke gabanta. Bisa namijin kokarin da aka yi cikin shekaru sama da 70 da suka wuce, kasar Sin ta yi nasarar daidaita matsalar abinci ga al’ummarta, kuma rayuwar al’ummar kasar ta ci gaba da inganta.Tun bayan taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar da ya gudana a shekarar 2012, kwamitin kolin jam’iyyar ya kuma mai da batun kiyaye tsaron abinci a matsayin babban aiki na farko wajen gudanar da harkokin kasar, inda yake jaddada cewa, “Ya kamata al’ummar Sinawa su samu abincin da za su ci a kullum”, ma’ana wato a kiyaye manufar dogara da kai wajen samar da abinci a gida.

Baya ga haka, yadda kasar take aiwatar da manufar kiyaye fadin gonaki da kuma bunkasa harkokin kimiyya domin kara samar da abinci, ya taimaka matuka wajen ciyar da al’ummar kasar. A kasar da ke da yawan al’umma wadda kuma ke fuskantar karancin filayen gona, kiyaye fadin gonaki na da matukar muhimmanci, don haka, kullum kasar Sin tana kiyaye fadin gonakinsu da ya kai a kalla kadada miliyan 730. A sa’i daya kuma, tana kokarin bunkasa harkokin kimiyya don kara samar da abinci, kasancewar filayen gona suna da iyaka, sabanin ilimi na kimiyya. Shinkafa muhimmin abinci ne ga kaso 60% na al’ummar kasar Sin, a shekarun 1970, marigayi Yuan Longping ya samu babban ci gaba a fannin nazarin fasahar noman shinkafar da aka tagwaita irinta, fasahar da ta taimaka ga samar da karin kaso 20% fiye da sauran nau’o’in shinkafa da ake nomawa. A cikin shekaru 30 da suka gabata, a kokarin da marigayi Yuan Longping da ‘yan tawagarsa suka yi, kasar Sin ta fita daga kangin karancin abinci.

Sharhi:Yadda kasar Sin take ciyar da al’ummarta biliyan 1.4_fororder_微信图片_20210530213949

Na uku, al’ummar Sinawa sun kuma amfana da manufofin kasar da ke kiyaye tsaron abinci a kowa ne lokaci. Kwanan baya, Vicent Nwanma, shehun malami a jami’ar Lagos ya wallafa wani sharhi mai taken “Food Security, lessons from China, Yuan Longping, inda ya bayyana cewa, kwalliya ta biya kudin sabulu yadda marigayi Yuan Longping ya cimma nasarar nazarin fasahar noman shinkafa da aka tagwaita irinta, sai dai abu mafi muhimmanci shi ne yadda aka kiyaye aikinsa bisa ga manufofi da tsare-tsare na kasar, sabili da yadda ake bukatar aiki mai dorewa wajen cimma wannan babbar nasara, ga shi kuma kasar Sin ta samar da kyakkyawan yanayi ga marigayi Yuan Longping wajen gudanar da aikinsa. Abin haka yake, a watan Faburairun wannan shekara, kwamitin kolin JKS ya fitar da takarda ta farko a wannan shekara game da farfado da kauyuka da ma gaggauta bunkasa ayyukan gona da raya kauyuka na zamani, takardar da ta mai da batun kiyaye tsaron abinci a wani matsayi mai matukar muhimmanci. A hakika, a cikin shekaru 18 a jere da suka wuce, kusan dukkan takardun da kwamitin kolin JKS ya fitar a farkon shekarun, sun kasance suna mai da hankali ne a kan batun ayyukan gona da kauyuka da ma manoma, matakin da ya tabbatar da bunkasuwar ayyukan gona da ma kauyuka a nan kasar, wanda kuma ya aza harsashi mai inganci ga kiyaye tsaron abinci a kasar.

Bisa kokarin da ya yi, ba kawai kasar Sin ta kai ga ciyar da al’ummarta ba, har ma tana kokarin taimaka wa sauran kasashe masu tasowa wajen daidaita matsalar abinci. A cikin ‘yan shekarun baya kuma, kasar Sin ta tura dimbin masana da kwararru zuwa kasashen Asiya da na Afirka da Latin Amurka da kuma yankin Carribean da na tekun Pasifik, don samar da gudummawa gwargwadon karfinta, lamarin da ya sa ta kasance kasa mai tasowa da ta fi yawan samar da kudade da tura kwararru karkashin tsarin hadin gwiwar kasashe masu tasowa na kungiyar abinci da aikin gona ta MDD.(Lubabatu)