logo

HAUSA

Yuan Longping, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen neman kawar da yunwa a duniya

2021-05-30 21:42:05 CRI

Yuan Longping, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen neman kawar da yunwa a duniya_fororder_微信图片_20210530213949

A ranar Asabar 22 ga watan Mayun shekarar 2021 ne, Masanan kimiyyar nan na kasar Sin Yuan Longping, mutumin da ya shafe tsawon rayuwarsa yana bincike, ya taimaka wajen ciyar da kasar mafi yawan al'umma a duniya ya mutu.

Yuan, wanda sunansa ya karade kasar Sin baki daya, ya yi suna wajen tagwaita irin shinfaka irinsa na farko, inda ake samun yabanya mai tarin yawa. 

Bayan ya shafe sama da shekaru 50 yana gudanar da bincike a fannin tagwaita irin shinkafa, malami a cibiyar nazarin aikin injiniya, ya taimakawa kasar Sin a gagarumin aikin ciyar da kusan kaso 1 bisa 5 na al'ummar duniya, da kasa da kaso 9 cikin 100 na filin noma a duniya.

A kasance tare da mu a shirin Allah Daya Gari Bamban don jin karin bayani dangane da tarihin marigayin da ma gaggarumar gudummawar da ya bayar wajen samar da abinci a duniya.(Lubabatu)