logo

HAUSA

Yadda ake raya harkoki ta wasu sabbin fasahohi a gundumar Chun’an

2021-05-30 21:32:33 CMG

Yadda ake raya harkoki ta wasu sabbin fasahohi a gundumar Chun’an_fororder_20210530-Bello-Sharhi

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya jaddada manufar kasar wajen neman ci gaban kasa ta hanyar kirkire-kirkire da samar da sabbin fasahohi yayin wani muhimmin taro na masu nazarin kimiya da fasaha na kasar, wanda ya gudana a ranar Juma’ar da ta gabata. Hakika neman raya kasa ta hanyar kirkire-kirkire daya ne daga cikin manyan manufofin kasar Sin. A shekarun 1980, yadda jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin dake kan karagar mulki a kasar ta kirkiro “tsarin gurguzu mai sigar musamman na kasar Sin” ya sa kasar samun ci gaban tattalin arziki cikin sauri matuka. Ma iya cewa, ba don kirkire-kirkiren da kasar Sin ta yi ba, to, ba za ta samu damar zama kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya ba. Sa’an nan wata ziyarar da na kai gundumar Chun’an dake lardin Zhejiang na kasar, ta sa na fahimci yadda manufar kirkire-kirkire take yin tasiri kan ayyukan raya kauyuka na kasar.

Gundumar Chun’an ta shahara bisa yadda ake samun babban tabki na Qiandao a can. Wannan babban tabki da fadinsa ya kai kilomita 567.4 yana janyowa gundumar dimbin masu yawon shakatawa. Sai dai, ba ko ina ne cikin gundumar Chun’an ake iya ganin muhalli mai ni’ima na tabkin Qian Dao Hu ba. Misali kauyen Xia’jiang wani karamin kauye ne, inda ba a samun ganin tabkin, kana wanda ya taba fama da talauci a lokacin baya. Amma yanzu kusan dukkan mazauna kauyen na iya mallakar kananan otel-otel na kansu, inda ake saukar da dimbin mutane masu yawon bude ido a ko wace rana. Ko a shekarar 2020, wani lokacin da aka fi fama da tasirin cutar COVID-19 a kasar Sin, an samu kimanin baki dubu 770 da suka ziyarci kauyen.

Dalilin da ya sa ake iya samun nasara a fannin raya aikin yawon shakatawa a kauyen Xia’jiang shi ne, domin mazauna kauyen sun kafa wata kungiyar hadin gwiwa don kula da harkokin kananan otel-otel dinsu. Ta wannan hanya, sun samu inganta aikin samar da hidimomi, da taimakawa wasu dattawan kauyen wajen kula da otel-otel don karbar baki. Wannan sabuwar dabarar da mutanen kauyen Xia’jiang suka kirkiro ta samu amincewa daga mutanen sauran kauyuka, lamarin da ya sanya wasu kauyuka 25 shiga kungiyar hadin gwiwa ta kauyen Xia’jiang, inda suke kokairn tsara wasu sabbin dabaru tare don samar da karin kudin shiga ga mutanen kauyukan.

Ban da wannan kuma, a gundumar Chun’an, ana kokarin kirkiro wasu sabbin dabaru masu alaka da masana’antu. Misali, a kauyen Lin’qi an  samu raya aikin samar da magungunan gargajiya sosai, har ma ya zama wani shahararren wurin da ake samar da magunguna masu inganci matuka. A cikin kauyen na ziyarci rumfar noman ganyayen magani, da wurin sarrafa magunguna, da kasuwar magani, gami da wani wurin nuna tarihi da al’adu masu alaka da maganin gargajiya. Madam Xu Juanfang, ita ce jami’a mai kula da kauyen. Ta gaya mana cewa, dabarar kauyenta wajen neman ci gaba, ita ce gabatar da wasu ganyayen magani masu daraja da inganci, sa’an nan an kara nomansu, da kafa masana’antar sarrafa magani, da kasuwannin sayar da magani, da raya aikin yawon shakatawa mai alaka da kiwon lafiya, da dai sauransu. Inda suke daukar matakai daban daban, domin yin amfani da magungunan gargajiya wajen taimakawa manoman samun karin kudin shiga.

Sai dai yadda ake kokarin raya aikin yawon shakatawa ko kuma sha’anin samar da magani na bukatar samun ruwa mai tsabta. A wannan fannin, gundumar Chun’an ta yi kirkire-kirkire wajen tsabtar ruwan tabkin Qiandao.

A cikin tabkin, na gwada fasahar kama kifaye ta wasu manyan komaye. Wadannan kifaye za su iya zama abinci masu dadi. Kana yayin da ake kiwonsu a cikin tabki, suna ba da taimako a fannin tsabtace ruwa. An ce kananan kifayen da nauyinsu ya kai kilo daya za su iya cinye wasu ciyayi da za su iya gurbata ruwa da nauyinsu ya kai kilo 40, yayin da kifayen suke girma.

Kana a kauyen Anyang, dokta Mu Quan ta gabatar mana sabuwar fasahar noma ta hanyar kare ruwa. Inda ta hanyar tsara wasu shuke-shuken da ake nomansu a cikin gona, za a iya rage yin amfani da maganin kashe kwari, da takin zamani. Kana a gefen gonar an dasa wasu bishiyoyi na musamman don tace sinadarai masu guba daga cikin ruwa. Ta wannan sabuwar fasahar, manoma ba za su zuba kudi da yawa wajen sayen magani da takin zamani ba, kana za su iya samar da karin amfanin gona masu inganci, wadanda suke samun karbuwa sosai a kasuwa.

Sa’an nan a fannin samar da hidimomi, shi ma ana kokarin kirkiro wasu sabbin dabaru. Misali an kafa wani kamfani mai suna “Bankin kare muhalli” a gudumar Chun’an, da nufin “ajiye albarkatun muhalli cikin bankin, don cire kudi daga bisani”. Ma’anar wato ana yin amfani da wannan banki wajen sarrafa albarkatu kamar na ganoki, da itatuwa, da gidaje dake hannun manoma, wadanda ba su amfani da su, ta hanyar janyo jari daga wasu kamfanoni. Ta wannan dabara, ana samun sarrafa albarkatu cikin hikima, tare da baiwa manoma damar samun karin kudin shiga.

Ban da wannan kuma, a gundumar Chun’an, na ga yadda ake kirkiro sabbin fasahohi a fannin aikin bada ilimi. A kauyen Fuwen, wata makarantar firamare ta samu lakabin “makarantar kauye da ta fi kyan gani”. An shafa ma bangon ginin makarantar fenti masu launuka daban daban, inda idan an kalli makarantar daga nesa, za a ji kamar ana cikin wani mafarki ne. Ko da yake wannan makarantar tana da dalibai dari daya kawai, amma ana kokarin gwajin wasu sabbin tunanin koyar da ilimi a can. Inda aka maida makarantar wani babban wurin wasa na yara, ta yadda za su iya girma ba tare da jin matsin lamba ba, don sanya su kaunar ilimi da binciken duniyar da muke zama a ciki.

Kirkiro sabbin fasahohi kamar wani aiki ne mai wuya, amma tushensa shi ne kokarin tunanin wasu sabbin dabaru don neman samun ci gaba, da dacewa da canzawar muhalli. Duk wani kokarin da ake yi na kirkiro sabbin fasahohi ana yinsa ne domin neman kyautata zaman rayuwar jama’a. Wannan shi ne dalilin da ya sa Sinawa suke matukar martaba aikin kirkiro sabbin fasahohi, kana dalili ne da ya sa kasar Sin ke kara samun ci gaba. (Bello Wang)

Bello