logo

HAUSA

Ba zai yiyu ‘yan siyasar Amurka su boye yunkurin illata kwanciyar hankalin HK ba

2021-05-29 16:21:32 CRI

Ba zai yiyu ‘yan siyasar Amurka su boye yunkurin illata kwanciyar hankalin HK ba_fororder_amurka

Sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken, ya fitar da wata sanarwa a ranar 27 ga wata, game da “daftarin shirin kyautata ka’idar zabe na shekarar 2021” da hukumar tsara dokoki ta yankin musamman na Hong Kong ta zartas, inda ya soki daftarin, yana mai cewa ya kayyade hakkin gudanar da harkokin yankin ga mazaunansa, haka kuma ya kayyade hanyoyin bayyana ra’ayoyinsu.

Hakika matakin da Amurka ta dauka bai zarce zaton al’ummun kasashen duniya ba, saboda har kullum wasu ‘yan siyasar kasar na yada labaran karya idan suka ga yankin Hong Kong ya samu ci gaba wajen gina tsarin demokuradiyya.

Amma karairayin ba za su taba zama gaskiya ba. Duk da cewa, ‘yan siyasar Amurka suna amfani da kalmomin demokuradiyya ko zaman walwala ko kuma hakkin bil Adama, ko shakka babu ba zai yiwu su boye yunkurinsu na illata yanayin kwanciyar hankalin da yankin Hong Kong ke ciki ba. Haka kuma matakin da suka dauka ya kara nuna cewa, aihinin burinsu shi ne, tsoma baki cikin harkokin Hong Kong, da ma harkokin kasar Sin baki daya, a maimakon kare demokuradiyya da hakkin bil Adama a yankin, da suke ikirari.(Jamila)