logo

HAUSA

Asusun IMF ya yabawa kasar Sin bisa kara kaimi ga aikin riga kafi a gida da waje

2021-05-29 15:51:45 CMG

Asusun IMF ya yabawa kasar Sin bisa kara kaimi ga aikin riga kafi a gida da waje_fororder_k

Babbar Manajar Asusun Bada Lamuni na Duniya IMF, Kristalina Georgieva, ta yabawa kasar Sin bisa kokarinta na kara kaimi ga aikin yin riga kafin COVID-19 a ciki da wajen kasar, tana mai cewa, dabarar yaki da annobar, ita ce dabara mafi dacewa ta bunkasa tattalin arziki.

Kristalina Geogieva, ta bayyana haka ne a jawabinta na bude tarukan lokacin bazara na kungiyar nazarin hada-hadar kudi ta kasa da kasa mai hedkwata a birnin Beijing na kasar Sin.

A cewarta, dole ne a yi wa akalla kaso 40 na al’ummar dukkan kasashe riga kafi, zuwa karshen shekarar 2021 da kuma akalla kaso 60 zuwa tsakiyar shekarar 2022.

Shugabar asusun na IMF ta kara da cewa, ingantaccen tsari da isassun kudi da gudunmuwar riga kafi da kara zuba jari don tabbatar da kaucewa komawar hannun agogo baya dangane da nasarar da aka samu kan annobar, za su lakume kusan biliyan 50 a duniya, tana mai cewa, gaggauta riga kafi kuma, ka iya kai wa ga samarwa duniya dala triliyan 9 daga yanzu zuwa shekarar 2025.

Ta ce kokarin kasar Sin na samar da riga kafi ga kasashen waje da kara kaimin yin riga kafin a gida, ya cancanci yabo. (Fa’iza Mustapha)

Faeza