logo

HAUSA

Kasar Sin na jagorantar duniya a fannin tashoshin fasahar sadarwa ta 5G

2021-05-27 11:10:45 CRI

Kasar Sin na jagorantar duniya a fannin tashoshin fasahar sadarwa ta 5G_fororder_微信图片_20210527133347

Kasar Sin ta jagoranci duniya wajen raya fasahar 5G, inda kawo yanzu, ta gina tashoshin fasahar 819,000, wanda ya dauki sama da kaso 70 na jimilar ta duniya baki daya.

Mataimakin ministan masana’antu da fasahar sadarwa na kasar Sin, Liu Liehong ne ya bayyana alkaluman, yayin taron baje kolin masana’antun manyan bayanai wato Big Data na kasa da kasa na kasar Sin dake gudana a Guiyang, babban birnin lardin Guizhou dake kudu maso yammacin kasar.

A cewar Liu Liehong, adadin mahadar sadarwar 5G a kasar Sin ya zarce miliyan 310, kwatankwacin kaso 80 na jimilar ta duniya baki daya.

Yayin shirin raya kasa na shekaru 5-5, karo na 13 tsakanin shekarar 2016 zuwa 2020, kasar Sin ta gina tsarukan fasahar 4G da wayoyin sadarwa na optical-fibre mafi girma a duniya, inda kaso 99 na kauyukan dake fadin kasar ke cin gajiyar fasahohin biyu.

A cewar kwamitin shirya taron, baje kolin na yini 3 da aka kaddamar a ranar Laraba, wanda ya ja hankalin kamfanoni 225 daga ciki da wajen kasar Sin, na gabatar da ingantattun nasarori da kirkire-kirkire a fannin kimiyya da fasaha na zamani. (Fa’iza Mustapha)