logo

HAUSA

Yawan Kudin Da Aka Samu Daga Tsarin Tauraron Dan Adam Na Beidou Ya Zarce Yuan Biliyan 400

2021-05-27 14:35:15 CRI

Yawan Kudin Da Aka Samu Daga Tsarin Tauraron Dan Adam Na Beidou Ya Zarce Yuan Biliyan 400_fororder_0527-beidou

An bude taron shekara-shekara na tauraron dan Adam dake ba da jagoranci kan zirga-zirga na kasar Sin karo na 12 a birnin Nanchang dake lardin Jiangxi na kasar Sin bisa taken “Yadda fasahohin zamani na sararin samaniya za su kyautata yanayi a nan gaba”. Tun bayan kaddamar da tsarin bada jagorancin zirga-zirga na tauraron dan Adam na Beidou-3 a karshen watan Yuli na bara, ya zuwa yanzu an yi amfani da tsarin a kasashe da yankuna fiye da 120 na duniya. Bayan barkewar yaduwar cutar COVID-19, kasashen duniya sun ci gaba da yin hadin gwiwa ta hanyar tsarin Beidou, kana an gaggauta aikin shigar da tsarin cikin kungiyoyin kasa da kasa.

A jawabin da ya gabatar yayin bikin bude taron shekara-shekara na tauraron dan Adam dake ba da jagorancin zirga-zirga na kasar Sin karo na 12, shugaban kwamitin kula da tsarin tauraron dan Adam dake bada jagoranci kan zirga-zirga na kasar Sin He Yubin ya bayyana cewa, bayan da aka kaddamar da tsarin Beidou-3 a karshen watan Yuli na bara, a karon farko Sin ta riga ta kafa tsarin sarrafa tauraron dan Adam na Beidou na musamman na kasar Sin, ana kuma amfani da tsarin a kasashen waje. Ya ce, “Bincike na nuna cewa, ana aiwatar da tsarin Beidou yadda ya kamata, wanda ya kasance a kan gaba a duniya. Ya kamata a kara hade fasahohin tauraron dan Adam na Beidou da sabbin fasahohi, don samar da sabon tsari ko sha’ani a wannan fanni. A shekarar 2020, yawan kudin da aka samu daga tsarin Beidou a kasar Sin, ya zarce Yuan biliyan 400. Kana an gaggauta yin amfani da tsarin a kasashen waje, yanzu kasashe da yankuna fiye da 120 a duniya suna amfani da tsarin.”

He Yubin ya yi nuni da cewa, a halin yanzu, ana kokarin raya kimiyya da fasaha da kuma wannan sha’ani a sabon zagaye a duniya, sha’anin bada jagoranci kan zirga-zirga ta tauraron dan Adam, ya shiga sabon lokaci na yin kirkire-kirkire. Don haka ya kamata a kara yin kirkire-kirkire da bude kofa da yin hadin gwiwa da amfani da wannan dama, ta yadda za a kara inganta tsarin Beidou zuwa sabon matsayi. Mr. He ya bayyana cewa, “Tarihi ya nuna cewa, rufe kofa zai hana samun ci gaba, bude kofa zai samar da karin abokai, da samun moriya tare. A don haka, ya kamata mu kara bude kofa ga kasashen waje, da yin hadin gwiwa a fannin kirkire-kirkire, da bullo da sabon tsari ta hanyar yin amfani da fifikon juna, don sa kaimi ga raya sha’anin tauraron dan Adam dake bada jagoranci kan zirga-zirga na duniya baki daya.”

Mataimakin shugaban ofishin kula da tsarin tauraron dan Adam dake bada jagoranci kan zirga-zirga na kasar Sin Yang Jun ya bayyana cewa, a halin yanzu, akwai taurarin dan Adam 45 dake bin hanyoyin tafiyarsu, daga cikinsu akwai na Beidou-2 guda 15, da na Beidou-3 guda 30, dukkansu suna aiki yadda ya kamata, tsarin Beidou mai alamar musamman ta kasar Sin, yana tabbatar da aikin taurarin dan Adam yadda ya kamata. Yang ya ce, “Tsarin Beidou yana kan gaba, ma’auninsa da aikinsa da kuma hidimar da ake samarwa ta tsarin, babu kamarsu a duniya.”

Yang Jun ya bayyana cewa, bayan da aka samu yaduwar cutar COVID-19, tsarin Beidou ya taimakawa kasashen duniya yin hadin gwiwa a fannoni daban daban ta yanar gizo. Yang ya bayyana cewa, “Bisa tsarin ganawa tsakanin firaministan Sin da na kasar Rasha, Sin da Rasha sun tsara shirin hadin gwiwa kan tauraron dan Adam dake bada jagoranci kan zirga-zirga daga shekarar 2021 zuwa 2025, da kuma sa kaimi ga yin gwaji, da kafa tasoshi, da inganta aikin noma ta tsarin a kasashen biyu. Kana Sin ta yi mu’amala tare da kasar Amurka a wannan fanni, da kuma daddale takardar fahimtar juna tare da kasar Argentina don yin hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu, wajen kafa tasoshin sa ido da yin bincike. Kana Sin ta shiga dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da ASEAN kan amfani da tsarin Beidou, yanzu haka ana amfani da tsarin a kasashe membobin kungiyar ASEAN.”(Zainab)