logo

HAUSA

Kasar Sin tana kara nuna sahihancin kawancenta da nahiyar Afirka

2021-05-26 09:20:11 CRI

A kwanakin baya ne, aka gudanar da taruka a matakai daban-daban da nufin taimaikawa wajen farfado da kasashen Afirka bayan yaki da annobar COVID-19 dake ci gaba da addabar wasu sannan duniya, da tabbatar da zaman lafiya da kuma tsaro.

Kasar Sin tana kara nuna sahihancin kawancenta da nahiyar Afirka_fororder_210526世界21019-hoto1

Irin wadannan taruka sun hada da taron tattara kudaden zuba jari a Afirka da ya gudana a kasar Faransa, inda mataimakin firaministan kasar Sin Han Zheng ya bayyana cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taba bayyana cewa, kawancen Sin da Afrika na da makoma iri daya. Kuma tun barkewar cutar COVID-19 a duniya, Sin take kokarin taimakawa Afrika.

Sauran tarukan sun hada da na kwamitin sulhun MDD, inda ministan harkokin wajen Sin, Wang Yi ya halarta ta kafar bidiyo, yayin da kasar Sin ke shugabantar kwamitin na watan Mayu. A duk irin wadannan taruka da sauransu, kasar Sin tana kara jaddada muhimmancin cika alkawarun da aka yi na taimakawa Afirka samun ci gaba, da magance matsalolin da suke damunta, ba tare da tsoma baki a harkokin cikin gidanta ko gindaya wani sharadi na siyasa ba.

Kasar Sin tana kara nuna sahihancin kawancenta da nahiyar Afirka_fororder_210526世界21019-hoto2

Kasar Sin na nanata cewa, yayin da ake kokarin tinkarar wannan annoba tare, abu mai muhimmanci shi ne farfadowa da raya Afrika, game da hakan, Sin ta gabatar da shawarwari hudu, wato na farko cika alkawarin da aka yi don tallafawa Afrika sassauta matsin da take fama da shi ta fuskar basussuka.

Wannan ya kara nuna sahihancin kasar Sin, na kara taimakawa kawayenta na kasashen Afirka amfana da kwarewa da ci gabanta,kamar yadda masu iya magana ke cewa, wai da abokin daka ake shan gari.

Bugu da kari, yayin taron hukumar lafiya ta duniya, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya zayyana irin gudummawar da kasar Sin ta bayar da wadanda take shirin bayarwa a fannoni daban-daban, duk da nufin raya Afirka, da tabbatar da zaman lafiya da tsaro a kasashen nahiyar, da magance matsalar sauyin yanayi, da kare muhalli da sauransu.(Saminu,Ibrahim/Sanusi Chen)