logo

HAUSA

Matsalar Nuna Bambancin Launin Fata Na Ci Gaba Da Tsananta A Amurka Lokacin Da Ake Cika Shekara Daya Da Mutuwar George Floyd

2021-05-26 20:42:10 CRI

Daga Amina Xu

Ranar 25 ga watan Mayu na shekarar bara, George Floyd dan Amurka bakar fata ya mutu sakamakon danne masa wuya da wani dan sanda farar fata ya yi masa da gwiwar kafarsa har tsawon mintoci fiye da 9. A cikin shekarar da ta gabata, an rika yin zanga-zanga don nuna rashin jin dadi kan matsalar nuna bambancin launin fata, da yaki da amfani da karfin tuwo a aikin ‘yan sanda. Shin ko mutuwar George Floyd ta warware wannan matsala da Amurka ta dade tana fuskanta?

Ana sa ran dokar George Floyd kan harkokin ‘yan sanda, za ta taimaka wajen kyautata halin da ake ciki a wannan fanni, amma ana tafiyar hawainiya game da shawarwarin da ake yi a majalissar dokokin kasar. Shugaba mai ci Joe Biden, ya mai da ranar tunawa da mutuwar Floyd matsayin lokaci na karshe da za a zartas da ita, amma ba a samu wani ci gaba game da hakan ba. Wani abun ban dariya shi ne, wannan batu ya baiwa wasu ‘yan siyasar kasar damar yin wasan kwaikwayo irin na siyasa.

Shugaban majalisar wakilai Nancy Patricia Pelosi ta taba bayyanawa a fili cewa “Muna godewa George Floyd matuka, saboda yadda ya sadaukar da ransa wajen tabbatar da adalci”. To, ko mene ne hakikanin adalci a nan? Shin gurfanar da Derek Chauvin a gaban kotu shi ne adalci? A’a, idan an tafiyar da adalci a Amurka, George Floyd ba zai mutu ba, har ta kai ga ya zama hujja ga wasu ‘yan siyasa wajen yin wasan kwaikwayonsu.

Wani abu mai tada hankali shi ne, ban da rashin adalci, matsalar bambancin launin fata na kan ganiyarta a Amurka. Mujallar “The Economist” ta kasar Birtaniya ta gabatar da rahoton jin ra’ayin jama’a dake cewa, yawan Amurkawa kashi 65% na ganin cewa, babu dangantaka mai kyau tsakanin al’ummu, kana kaso 59% sun nuna cewa, ‘yan sandan Amurka ba sa daidaita huldarsu da kananan al’ummu, yayin da aka samu wasu kaso 40%, dake ganin dangantakar ‘yan sanda da kananan al’ummu ta kara tsananta bayan mutuwar Floyd.

‘Yan siyasa sun gaza cimma burinsu na ganin mutuwar Floyd ta ba su damar shawo kan matsalar bambancin launin fata a kasar, sun rika gamsar da kansu karkashin abubuwa da suka yi game da wannan batu, amma ba alamu dake nuna yiwuwar warware wannan batu ko kadan.

Wani abu mai girgiza zuciya shi ne, bayan mutuwar Floyd, rikicin tsakanin al’ummu ya kara tsananta, har ma ra’ayin fararen fata dake zama gaban komai ya kara kunno kai. A ran 23 ga watan Afrilu, hukumar bincike ta Amurka ta sanar da shigar da kara kan masu kai hari kan majalissar dokoki 106. Kafin wannan kuma, an tsare mutane fiye da 400 a jihohi 42, bisa tuhumarsu da aikata laifi. Wani rahoto da hukumar ta fitar na nuna cewa, a cikin wadannan mutane 500, yawancinsu masu ra’ayin Nazi a sabon salo, da ra’ayin murdiya da masu bibbiyar kungiyar 3K mai tsatsaruran ra’ayi, wadanda suke nacewa ga tunanin fararen fata na gaban komai ne. Ana iya cewa, adalcin da ake samu bisa sadaukar da ran Floyd ta bakin wasu ‘yan siyasa yana tsananta rikici tsakanin al’ummun kasar, har ma ya kai ga haifar da bambancin launin fata, da tunanin fararen fata gaban komai.

Kowa na iya ganin cewa, ba a kai ga kyautata matsalar bambancin launin fata a Amurka ba bayan mutuwar Floyd ba. A maimakon haka tunanin fararen fata a gaban komai na kunno kai, yayin da ‘yan siyasa ke kokarin wasan kwaikwayonsu ba tare da nuna kunya ba. A ko wane watan Mayu, Amurka za ta shiga watan ‘yan Amurka masu asalin Asiya, bisa yadda aka sabawa za a yi bukukuwan murnar hakan, don nuna godiya ga gudunmawar da wadannan mutane suka bayar wajen raya al’ummar, da ingiza fahimtar al’ummu. Sai dai kuma ana nuna kyamar Amurkawa 'yan asalin Asiya,matakin da ya kai ga kai musu hari, da aikata laifuffuka kan su, wanda hakan ya sa wadannan rukuni na mutane suke rayuwa cikin tsaro da fargaba, kuma babu tabbacin kare hakkinsu a ko da yaushe.

Hakan shi ne hakikanin halin da ake ciki a Amurka. Kamar yadda mai masaukin shirin NBC ya fadi a cikin wani shirinsa: Ko ‘yan sanda suna amincewa da a yi musu bincike, abin da ya nuna cewa ana samun ci gaba a fannin gudanar da harkoki bisa doka, da tabbatar da hakkin jama’a ko lafiyar bakaken fata? Bari in gaya muku gaskiya, ba a yin hakan. (Amina Xu)