logo

HAUSA

Bai dace Amurka ta soki sauran kasashe ba kasancewar ita kanta ta gaza a fannin dakile nuna wariyar launin fata

2021-05-26 20:13:53 CRI

Bai dace Amurka ta soki sauran kasashe ba kasancewar ita kanta ta gaza a fannin dakile nuna wariyar launin fata_fororder_1

Jiya Talata 25 ga watan nan bisa agogon kasar Amurka, an gudanar da wasu ayyuka iri daban daban a sassan kasar, domin nuna juyayin rasuwar George Floyd, ‘dan asalin Afirka wanda ya mutu shekara daya da ta gabata, a sanadin kisan gillar da wani ‘dan sanda farar fata ya yi masa.

Duk da cewa, an riga an yankewa ‘dan sandan hukunci bisa laifin da ya aikata, amma al’ummun kasar ta Amurka suna ci gaba da nuna adawa da kyama, bisa wariyar launin fata da ta dade tana faruwa a kasar. Kana abun bakin ciki shi ne, bayan rasuwar George Floyd, ba ma kawai laifuffukan da ‘yan sandan kasar suke aikatawa yayin da suke gudanar da aiki ta hanyar nuna karfin tuwo na karuwa ba ne, har ma ana kara ba da kariya ga ‘yan sandan.

Jiya an wallafa wani rahoto mai taken “Yan sanda suna ci gaba da kashe mutane kamar yadda suka yi a baya” a shafin yanar gizon watsa labaran siyasa na Amurka wato Politico, kuma mujallar “Time” ta kasar, ita ma ta wallafa rahoton dake cewa, duk da cewa yawancin al’ummun kasar suna zaune a cikin gida sakamakon yaduwar annobar cutar COVID-19, amma alkaluman binciken da aka fitar sun nuna cewa, tun daga watan Yunin shekarar 2020, adadin mutanen da ‘yan sandan Amurka suka kashe, ya yi daidai da adadin da suka kashe a cikin shekaru biyar da suka gabata. Har ma an nuna cewa, tun daga farkon shekarar bana zuwa ranar 30 ga watan Afirilun bana, kwanaki 6 ne kacal aka samu ‘yan sandan Amurka ba su kashe mutane ba. Haka zalika, an lura cewa, a cikin mutane 1,126 da ‘yan sandan Amurka suka kashe a cikin shekarar 2020, kaso 28 cikin dari ‘yan asalin Afirka ne.

A zahiri nuna wariyar launin fata tana ci gaba da yaduwa a Amurka cikin tsawon shekaru dari daya. Abun tambaya shi ne ina dalilin da ya sa Amurka take ci gaba da sukar sauran kasashe, game da batun kare hakkin dan Adama? Idan tana son koyar da saura yadda ya dace su kare hakkin dan Adam, to dole ne ita kanta ta daidaita matsalar kafin saura, shi ya sa a kan ce, bai dace Amurka ta soki saura kan batun kare hakkin dan Adam ba. (Jamila)