logo

HAUSA

Firaministan Sin ta yi kira da a kara karfin kasuwa don samun ci gaba

2021-05-26 13:05:23 CRI

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya jaddada bukatar kara kaimi, don kara yin gyare-gyare da bude kofa, da kara karfin kasuwa, da magance sauye-sauyen da ake samu a cikin gida da kuma waje, don ciyar da bunkasuwar tattalin arzikin kasar mai inganci zuwa gaba.

Li, wanda har ila mamban zaunannen kwamitin hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na JKS, ya bayyana haka ne, yayin rangadin duba birnin Ningbo a lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin da ya gudanar daga ranar Litinin zuwa jiya Talata.

Yayin da ya ziyarci tashar ruwa ta Ningbo-Zhoushan, wani babban yankin yada zango na manyan hajoji a kasar Sin, kira ya yi da a kara mayar da hankali kan sauye-sauyen da tattalin arzikin duniya ke fuskanta, da yadda farashin kaya ke sauyawa a kasuwannin duniya.

Ya kara da cewa, ya kamata kasar Sin ta kara fadada bude kofarta, da kara saukaka yadda kwastam suke tantance kaya, da gudanar da cinikayya mai tsafta da adalci. Ya kara da cewa, ya kamata kasar Sin ta taka cikakkiyar rawa da za ta taimakawa tashar ruwar cin gajiyar tsare-tsare na kasuwa, da zai inganta yadda ake shigo da kayayya, da adanawa da kuma cinikayyar manyan hajoji.(Ibrahim)