logo

HAUSA

An tusa keyar shugaban rikon kwaryar Mali da firaministan kasar zuwa sansanin sojan Kati da karfin tsiya

2021-05-25 10:37:16 CRI

An tusa keyar shugaban rikon kwaryar Mali da firaministan kasar zuwa sansanin sojan Kati da karfin tsiya_fororder_Mali

Rahotanni daga kasar Mali na cewa, an garzaya da shugaban rikon kwaryar kasar Bah N’Dawa da firaministan kasar Moctar Ouane da karfin tsiya zuwa sansanin soja na Kati, bayan da aka sanar da mambobin sabuwar gwamnatin kasar da maraicen jiya.

Kafofin watsa labaran kasar na cewa, wannan mataki ba zai rasa nasaba da rashin amincewar tsohon kwamitin ceton jama’ar kasar(CNSP) ba, biyo bayan cire mambobinta biyu, wato kanar Sadio Camara, tsohon ministan tsaro da kula da harkokin yan mazan jiya, da kuma kanar Modibo Kone, tsohon ministan tsaro da kare fafaren hula daga cikin sabuwar gwamnatin da firaministan ya kafa.

A cewar wasu majiyoyi dake kusa da sojojin kasar, mutanen biyu, na daga cikin wadanda suka kitsa boren sojojin da suka kai ga kifar da shugaba Ibrahim Boubacar Keita a ranar 18 ga watan Agustan shekarar da ta gabata.

Ana dai zargin kanar Modibo Kone ne, saboda karuwar rashin tsaro a kasar, musamman a birnin Bamako. Sai dai kuma, an yaba yadda kanar Sadio Camara yake taka-tsan-tsan kan irin rawar da ya taka, da ma yadda ya kai wannan matsayi a rundunar sojojin kasar. Masu sharhi da dama dai, sun yi mamakin ficewarsa daga cikin gwamnati. (Ibrahim)