Fasahar noma irin shinkafa da aka tagwaita ta taimaka ga kara samar da abinci a kasar Madagarscar
2021-05-25 14:47:36 CRI
Fasahar noman irin shinkafa da aka tagwaita ba kawai ta amfana wa kasar Sin ba, a hakika, tana kuma amfana wa kasashen Afirka. A kasar Madagarscar, yanzu haka ana kokarin yayata fasahar, inda gwamnatin kasar take fatan yin amfani da fasahar wajen magance matsalar karancin abinci da take fuskanta, don sa kaimi ga ci gaban ayyukan gona da kuma kyautata rayuwar al’umma. Abokiyar aikinmu Lubabatu na dauke da karin haske.
Watan Mayun kowace shekara lokaci ne da ake aikin girbin shinkafa a kasar Madagarscar. Kididdigar da ma’aikatar noma ta kasar Madagarscar ta fitar ta yi nuni da cewa, an yi girbi mai armashi a wannan shekara, inda aka samu karin shinkafar da ta zarce tan dubu 150.
Tun daga shekarar 2007, kamfanin raya ayyukan gona na kasa da kasa na Yuan dake lardin Hunan na kasar Sin, ya fara tura kwararru zuwa kasar ta Madagarscar don yayata fasahar noman irin shinkafar da aka tagwaita. Bisa kokarin da aka yi cikin fiye da shekaru 10 da suka wuce, Madagarscar ta zamanto kasar da ta fi yawan filayen noman irin shinkafar da aka tagwaita da ma kasar da ta fi yawan samar da shinkafar a nahiyar Afirka. Madam Li Yanping, wadda ke kula da ayyukan noman shinkafar da fasahar tagwaita irinta ta bayyana cewa,“Kawo yanzu, fadin gonakin da ake noman irin shinkafar da aka tagwaita a kasar Madagarscar, ya zarce kadada dubu 50. Daga cikin manyan shiyyoyin kasar, sama da rabi ana noman nau’in shinkafar. A bara, ma’aikatar aikin gona ta kasar, ta sayo ire-iren nau’in shinkafar kimanin tan 500 daga kasar Sin, don habaka noman nau’in shinkafar a kasar, a kokarin kara samar da abinci a kasar.”
Madagarscar tana da dogon tarihi na noman shinkafa, kuma shinkafa ta kasance muhimmin abincin al’ummar kasar. Baya ga haka, kasar tana da yanayin mai kyau na noman shinkafa. Sai dai a sa’i daya, nau’o’in shinkafar sun lalace a kasar, inda ake iya samun shinkafa kimanin tan 3 ne kawai da aka noma a gonakin da fadinsu ya kai kadada guda, matsalar da take habaka gibin abinci a kasar. Don haka, gwamnatin kasar da al’ummarta suna matukar bukatar kara samar da shinkafa ta hanyar yayata fasahar tagwaita irin shinkafa, don biyan bukatun al’umma ta fannin abinci.“Alkaluman da ma’aikatar ayyukan gona ta kasar Madagarscar ta fitar sun yi nuni da cewa, ana iya samar da kimanin tan 2.8 na ainihin nau’in shinkafa ta kasar daga gonaki kadada guda, a yayin da ake iya samar da kimanin tan 6 zuwa 7 har ma 10 na nau’in shinkafa na kasar Sin a irin wadannan fadin gonakin, wanda ya ba da babbar gudummawa wajen warware batun samar da isashen abinci a kasar. Don haka, jami’an gwamnatin kasar da ma manoma duk sun nuna yabo ga shinkafar. Ministan aikin gona na kasar ya ce, fasahar noman shinkafar da aka tagwaita irinta ta taimaka sosai ga daidaita matsalar abinci da ma maido da kasar a matsayin kasar da ke fitar da shinkafa.”
Li Yanping ta ce, manoma da yawa na kasar na kokarin shiga kwasa-kwasai da kasar Sin ta samar, don fatan ganin rayuwarsu ta kyautata bisa ga noman shinkafar da fasahar tagwaita irinta.
Bayan rasuwar marigayi Yuan Longping a makon da ya gabata, ministan kula da ayyukan gona da kiwon dabbobi da aikinsu na kasar, Lucien Ranarivelo ya wallafa sakon jaje ta kafar twitter, inda ya ce, bisa sakamakon da aka kafa cibiyar nazarin fasahar tagwaita irin shinkafa, ya sa yawan shinkafar da aka samar a gonakin da fadinsu ya karu sosai. Ya ce,“Muna matukar bakin ciki game da rasuwar marigayi Yuan Longping, kuma rashinsa babbar hasara ce ga kasar Sin da ma duniya baki daya. Kasancewarmu abokan hadin gwiwarsa, mun kafa cibiyar nazarin fasahar tagwaita irin shinkafa. Marigayi Yuan Longping ya ba mu babbar gudummawa ta fannin cimma burin na kawar da matsalar yunwa da samar da isasshen abinci.”
Baya ga Madagarscar, an kuma yayata fasahar tagwaita irin shinkafa a kasashen Afirka da suka hada da Nijeriya, da Kenya, da Mozambique da sauransu, matakin da ya taimaka ga samar da isasshen abinci a kasashen. (Lubabatu)