logo

HAUSA

Shugaban WAHF: Marigayi Yuan Longping ya ba da babbar gudummawa wajen samar da isasshen hatsi ga kasar Sin da ma duniya baki daya

2021-05-24 15:08:27 CRI

Shugaban WAHF: Marigayi Yuan Longping ya ba da babbar gudummawa wajen samar da isasshen hatsi ga kasar Sin da ma duniya baki daya_fororder_WAHF

Ranar Asabar 22 ga wata ne, masanin kimiyyar nan na kasar Sin Yuan Longping, wanda ya yi fice wajen kirkiro fasahar tagwaita irin shinkafa na farko, wanda ya fitar da mutane da dama daga yunwa, ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 91, bayan fama da rashin lafiya. Game da wannan, Parviz Koohafkan, shugaban asusun kula da kayayyakin tarihi na aikin gona da aka gada daga kaka da kakani na duniya wato WAHF ya bayyana cewa, Marigayi Yuan Longping ya bayar da babbar gudummawa wajen samar da isasshen hatsi ga kasar Sin da ma duniya baki daya.

Parviz Koohafkan, shugaban asusun kula da kayayyakin tarihi na aikin gona da aka gada daga kaka da kakani na duniya wato WAHF ya taba aiki a hukumar abinci da aikin gona ta MDD ta FAO, ya kuma sha kawo ziyarar aiki kasar Sin a cikin shekaru fiye da 30 da suka gabata. Ya bayyana cewa, ya ga yadda kasar Sin ta samu nasara a fannin aikin gona. Ya hadu da Marigayi Yuan Longping a yayin taron FAO a shekarar 2004 wadda aka mai da shekarar a matsayin shekarar shinkafa ta duniya. A ganin Koohafkan, Marigayi Yuan wanda ya dukufa wajen nazarin fasahar tagwaita irin shinkafa, ya bayar da gagarumar gudummawa ga aikin kawar da kangin talauci da samar da isasshen hatsi a kasar Sin. Yana mai cewa,

“Na ga yadda kasar Sin ta canja daga kasa mai fama da talauci zuwa daya daga cikin kasashe mafiya ci gaba na zamani. Kasar Sin ta samu nasara wajen kawar da fatara, har ma muna iya dandana abincin Sin masu dadi a kasar Italiya. Aikin Marigayi Yuan Longping ya taimaka sosai ga yadda kasar Sin ta kau da talauci, har ma ya tabbatar da samun isasshen hatsi a kasar.”

Mr. Koohafkan shi ne ya kafa asusun WAHF, kana mutum na farko da ya gabatar da ra’ayin kiyaye muhimman kayayyakin tarihin aikin gona da aka gada daga kaka da kakani na duniya. Kuma kasar Sin, ita ce kasa ta farko da ta goyi bayan wannan ra’ayi, wadda kuma take da irin wadannan kayayyakin tarihi mafi yawa a duniya. Ya zuwa yanzu kasar na da kayayyakin tarihin aikin gona guda 15, ciki har da tsarin kasancewar noman shinkafa da kiwon kifaye gu daya dake Qingtian na lardin Zhejiang da dai sauransu. A shekarar 2004, Koohafkan ya taba tattaunawa da Marigayi Yuan kan wannan ra’ayin, yadda Yuan ya kula da kayayyakin tarihin aikin gona ya ba shi mamaki sosai. Ya ce,

“Shi masanin kimiyya ne dake da ilmi mai zurfi da ma son karbar ra’ayoyin zamani. Yayin da nake hira da shi a shekarar 2004, ya amince da aikin kiyaye kayayyakin tarihin aikin gona. Hakika ya gudanar da manyan ayyuka don tabbatar da samun dauwamammen ci gaban ayyukan gona, da samar da isasshen hatsi, da taimakawa wajen kau da talauci.”

Yanzu ana yayata fasahar tagwaita irin shinkafa sosai a kasashen Indiya, Bangladesh, Indonesiya, Vietnam, Philippines, Amurka, Brazil, Madagascar da dai sauransu, fadin gonakin da ake noman irin shinkafar ya kai hekta miliyan 8, matsakaicin yawan shinkafar da ake samu daga ko wace hekta, ya fi sauran nau’ikan shinkafa masu inganci yawa har kimanin tan 2. Mr. Koohafkan ya nuna cewa, shinkafa muhimmin abinci ne na Sinawa, ban da haka, muhimmin abinci ne na dimbin kasashen Asiya da Afirka. Marigayi Yuan Longping shi ma ya ba da babbar gudummawa ga aikin samar da isasshen hatsi a duniya. Ya kara da cewa,

“Aikinsa na da matukar muhimmanci, wanda ya samu manyan nasarori a fannin tabbatar da samar da isasshen hatsi. A matsayinsa na masanin kimiyya, ya ba da gudummawa ga cibiyar nazarin noman shinkafa ta duniya, inda ya horar da dimbin matasa. Yanzu duk duniya ta amince da gudummawar da ya bayar da sauran masanan ilmin kimiyyar fasahar tagwaita irin shinkafa suka bayar. Rasuwarsa wani babban rashi ne a duniya. Amma abin farin ciki shi ne, matasa za su ci gaba da yada fasahar da ya kirkira. A ganina, Marigayi Yuan ya ba da gagarumar gudummawa ga kasar Sin, kasashen Asiya, har ma da duniya baki daya.” (Kande Gao)