logo

HAUSA

Masanan Kasa Da Kasa Sun Yaba Nasarar Saukar Na’Urar Bincike Ta Zhurong Ta Kasar Sin A Duniyar Mars

2021-05-24 20:41:04 CRI

Masanan Kasa Da Kasa Sun Yaba Nasarar Saukar Na’Urar Bincike Ta Zhurong Ta Kasar Sin A Duniyar Mars_fororder_1

Daga Ahmad Fagam

Kamar yadda a karshen wannan mako hukumar kula da ayyukan sararin samaniya ta kasar Sin wato (CNSA) ta sanar cewa, na’urar binciken duniyar Mars ta kasar Sin wato Zhurong, ta yi tafiya a kan doron duniyar Mars daga inda ta sauka. Wannan nasarar tafiyar Zhurong ta farko, ta sa kasar Sin ta zama kasa ta biyu a duniya bayan kasar Amurka, da ta sauka tare da amfani da na’urarta a duniyar Mars. Bayanai sun nuna cewa, na’urar Zhurong ta ajiye tayoyinta a kan doron duniyar Mars ne da misalin karfe 10:40 na safiyar Asabar din da ta gabata agogon birnin Beijing. To ko me yasa saukar na’urar binciken ta kasar Sin a duniyar Mars ta janyo hankalin duniya?

Manazartan kasa da kasa da dama sun yi fashin baki tare da bayyana ra’ayoyinsu gami da nuna yabo kan wannan nasara. Alal misali, kamar yadda shafin Internet na mujallar kimiyya da fasaha ta Amurka wato Scientific American wacce ake wallafata wata wata, ta bayyana ra’ayinta kan samun nasarar saukar na’urar bincike ta Tianwen-1 ta kasar Sin a duniyar Mars a ranar 15 ga wannan wata, saukar na’urar binciken a duniyar Mars, wata sabuwar nasara ce da kasar Sin ta samu yayin da take aiwatar da shirinta na bincike a sararin samaniya, lamarin da ya gwada kuzarin kasar Sin wajen yin gwagwarmaya game da fadi-tashin bunkasa fasahohi ta hanyar bincike da nazari kamar yadda masu hikimar Magana ke cewa “ilmi kogi ne” a wani kaulin akan ce “zomo baya kamuwa daga zaune.” Saukar na’urar bincike ta Tianwen-1 mai dauke da karamar na’urar bincike ta Zhurong a duniyar Mars cikin nasara kuma kamar yadda ya kamata kana daidai yadda aka tsara, ya nuna cewa kasar Sin ta samu babban ci gaba a fannin binciken sararin samaniya tsakanin duniyarmu ta Earth da wata duniya ta daban, a maimakon duniyar wata kawai. Hakika, samun nasarar saukar na’urar bincike ta Tianwen-1 a duniyar Mars, ta shaida cewa, kasar Sin ta nakalci wasu fasahohi masu sarkakiyya dangane da saukar na’ura a duniyar Mars, musamman ma koda yake wannan shi ne karo na farko da kasar Sin ta fara binciken duniyar Mars. Ko shakka batu, saukar na’urar bincike ta Tianwen-1 a duniyar Mars, ba kawai ya kasance abin alfahari ne ga kasar Sin kawai ba, har ma yana da muhimmiyar ma’ana ga duk duniya baki daya. Babban abin farin ciki shine, sakamakon da aka samu a yayin gudanar da binciken a duniyar Mars zai kara tagomashi wajen bada damar gano wasu sabbin fasahohi wadanda za a iya amfani da su wajen kyautata zaman rayuwar dukkan bil adama. Ita ma hukumar kula da ayyukan sararin samaniyar Amurka NASA, ta taya murnar nasarar saukar na’urar binciken ta kasar Sin a duniya Mars, kamar yadda mataimakin shugaban hukumar ta NASA, Thomas Zurbuchen, ya bayyana a makon da ya gabata a sakon da ya aike don taya murnar nasarar saukar na’urar bincike ta kasar Sin mai suna Tianwen-1 a duniyar Mars. Cikin sakon nasa, Thomas Zurbuchen ya taya hukumar kula da ayyukan sararin samaniyyar kasar Sin CNSA murna, bisa nasarar da hukumar kula da ayyukan na’urar bincike ta kasar Sin Tianwen-1 ta samu inda karamar na’urar bincike ta Zhurong ta sauka cikin nasara a duniyar Mars don gudanar da aikin bincike. Babban abinda muke fata shine aikin zai samar da muhimmiyar gudunmawa ga ayyukan binciken duniyar Mars don baiwa dan Adam damar kara fahimtar waccar duniyar mai launin ja.(Ahmad Fagam)