logo

HAUSA

Kasar Sin ta dauki hakikanan matakan taimakawa kasashen Afirka cikin sahihanci

2021-05-23 16:57:15 CRI

A kwanan baya, kasar Sin, wadda ke shugabantar kwamitin sulhu na MDD a wannan wata na Mayu, ta ba da shawarar shirya taron mahawara bisa jigon “Tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Afirka: taimakawa kasashen Afirka wajen sake neman bunkasuwa da kawar da tushen haddasa rikice-rikice bayan annoba”. A yayin taron, Mr. Wang Yi, mamban majalisar gudanarwa, kana ministan harkokin wajen kasar Sin ya nuna cewa, “a gaban annoba, babu wata kasa da za ta iya gujewa annobar, har ma ta zama wani wurin da aka manta da taimakawa wajen dakile annobar.”

A yayin da kasar Sin ta samu nasarar dakile cutar numfashi ta COVID-19, amma galibin kasashen Afirka har yanzu suna cikin mawuyacin hali sakamakon rashin allurar rigakafi da sauran kayayyakin kandagarkin cutar, har ma tattalin arziki da yanayin kwanciyar hankalinsu sun shiga wani hali, a matsayinta na daya daga cikin mambobin dindindin na kwamitin sulhu na MDD, kuma aminiyar kasashen Afirka, kasar Sin ba ta yi shiru ba wajen magance halin da ake ciki, ta dauki matakan daidaita matsalolin da kasashen Afirka suke fuskanta ta hanyar yin hadin gwiwar bangarori daban daban. A makon da ya gabata, shugaban kasar Sin Xi Jinping, da Mr. Han Zheng, zaunannen mataimakin firaministan gwamnatin kasar, da Mr. Wang Yi, mamban majalisar gudanarwar kasar, kana ministan harkokin waje daya bayan daya sun ba da shawara ko halartar tarukan kasa da kasa game da yadda za a taimakawa kasashen Afirka wajen tinkarar annobar, da sake bunkasa Afirka bayan kawar da annobar, da kuma kawar da tushen haddasa rikice-rikicen da suke faruwa a kullum a nahiyar Afirka. A yayin tarukan, dukkansu sun gabatar da shawarwari, har ma fitar da hakikanin matakan taimakawa kasashen Afirka wajen tinkarar matsaloli iri iri da suke fuskanta. Wannan ya bayyana cewa, alkawarin sada zumunta tsakanin Sin da kasashen Afirka cikin sahihanci, ba wata maganar diflomasiyya kadai bane, har ma wani alkawari ne da kasar Sin ke kokarin cikawa.

Kasar Sin ta dauki hakikanan matakan taimakawa kasashen Afirka cikin sahihanci_fororder_210523-sharhi-Sanusi-hoto2

A fannin dakile cutar COVID-19, a kullum kasar Sin tana goyon bayan kasashen Afirka. Bayan barkewar annobar, tawagogin masu aikin jinya na kasar Sin 46 dake kasashen Afirka daban daban ba su yi kasa a gwiwa ba sun hanzarta kaddamar da aikin kandagarkin annobar, a yayin da sauran tawagogin masu aikin jinya na kasar Sin 15 sun yi rangadi a Afirka bisa gayyatar da gwamnatocin kasashen Afirka suka yi musu. Sannan an kafa tsarin yin hadin gwiwa tsakanin asibitocin kasar Sin 43 da takwarorinsu na Afirka. Bugu da kari, wasu kungiyoyin jin kai masu zaman kansu na kasar Sin ma sun samar wa kasashen Afirka fasahohi da shirye-shirye da kuma dimbin kayayyaki na kandagarkin annobar.

Har yanzu wasu kasashen yamma na tsayawa tsayin daka kan matsayinsu na “kare alluran rigakafin annobar” da “nuna banbanci kan batun samar da allurar”, ko shakka babu, kasar Sin ta nuna adawa da irin wannan mummunan matsayi. Kawo yanzu, kasar Sin ta riga ta samar wa kasashen Afirka fiye da 30 alluran rigakafin annobar bisa bukatun da suke da su.

Kasar Sin ta dauki hakikanan matakan taimakawa kasashen Afirka cikin sahihanci_fororder_210523-sharhi-Sanusi-hoto1

Kowa ya sani, a cikin shekaru 70 da suka gabata bayan kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin, a kullum kasar Sin na goyon bayan kasashen Afirka wajen neman ci gabansu, musamman a fannonin raya tattalin arziki da tabbatar da kwanciyar hankali a Afirka. A ’yan shekarun baya, kasar Sin da kasashen Afirka sun yi hadin gwiwa sun kaddamar da “shirye-shiryen hadin gwiwa 10” da “matakan aiwatar da shirye-shirye 8” wajen bunkasa tattalin arziki da tabbatar da zaman lafiya, da kyautata aikin ba da ilmi da kirkiro sabbin fasahohin kimiyya da kuma bunkasa aikin gona da dai makamatansu. A yayin taron muhawara mai jigon “Tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Afirka: taimakawa kasashen Afirka wajen sake neman bunkasuwa da kawar da tushen haddasa rikice-rikice bayan annoba”, kasar Sin da kasashen Afirka sun kasance tare sun nuna goyon baya ga “shawarar kafa abokantaka domin bunkasa Afirka”.

Bugu da kari, bayan barkewar annobar, a lokacin da kamfanoni masu jarin kasar Sin wadanda suke kasashen Afirka suke kokarin dakile annobar, sun yi kokarin shawo kan illolin da annobar ta kawo ga kasashen Afirka, ba su janye jari da ma’aikatansu daga Afirka ba, har ma ba su rufe kofofinsu da kuma rage yawan kayayyakin da suke samarwa ba. Sakamakon kokarinsu, a bara, sun gama wasu muhimman ababen more rayuwar jama’a da yawa, kamar layukan dogo da titunan mota, da filayen saukar jiragen sama da gonakin noman shinkafa da dai makamatansu wadanda suke da muhimmanci sosai wajen kyautata zaman rayuwar al’ummun Afirka.

Kasar Sin ta dauki hakikanan matakan taimakawa kasashen Afirka cikin sahihanci_fororder_210523-sharhi-Sanusi-hoto4

A waje daya kuma, kasar Sin na kokarin taimakawa kasashen Afirka wajen bunkasa masana’antu masu alaka da fasahohin zamani da kuma cimma burinsu a sararin samaniya. Mr. Tamidayo Oniosun , wani mai nazarin kimiyyar sararin sama, kuma wanda ke tafiyar da wani shafin intanet dake shafar labarun sararin samaniya, ya ce, “A kullum kasar Sin na taimakawa kasashen Afirka ta samar musu taurarin dan Adam na binciken sararin samaniya.” Alali misali, a watan Disamban shekarar 2019, kasar Sin ta taimaki kasar Habasha wajen harba wani tauraroin dan Adam, ta yadda kasar Habasha za ta iya yin amfani da wannan tauraroin dan Adam wajen yin hasashen yanayin duniya, da duba yanayin muhalli da yadda shuke-shuke suke girma. A watan Disamban shekarar 2020, kasar Sin ta sake taimakawa kasar Habasha wajen harba wani tauraron dan Adam daban.

Kasar Sin ta dauki hakikanan matakan taimakawa kasashen Afirka cikin sahihanci_fororder_210523-sharhi-Sanusi-hoto3

Dadin dadawa, a kullum kasar Sin tana bayar da gudummawarta sosai wajen tabbatar da kwanciyar hankali a Afirka. Kawo yanzu kasar Sin ta riga ta aika tawagogin jiragen ruwan yaki har sau 37 zuwa yankin teku na Aden domin tsaron jiragen ruwan kasuwanci na kasashen daban daban wadanda suke ratsa yankin. Ban da wannan kuma, yanzu akwai ma’aikatan kasar Sin 2043 da suke tabbatar da zaman lafiya a madadin MDD a kasashen Mali da Liberia da Sudan, da Sudan ta kudu, da kuma Kongo Kinshasa. Suna bakin aikinsu ba dare ba rana.

Nahiyar Afirka muhimmiyar mamba ce ga duk duniya. Idan tana da zaman lafiya da kwanciyar hankali, da kuma samun bunkasuwa a kullum, tabbas ne za ta bayar da muhimmiyar gudummawarta ga ci gaban bil Adam baki daya. Kasar Sin tana son yin hadin gwiwa da ’yan uwa na Afirka da abokai na sauran kasashen duniya domin taka rawarta wajen bunkasa Afirka da kuma kawo zaman lafiya a Afirka. Sakamakon haka, kasar Sin da kasashen Afirka za su iya bayar da gudummawarsu tare wajen gina zaman al’ummar bil Adama dake da kyakkyawar makoma a duk duniya.  (Sanusi Chen)