logo

HAUSA

An musunta jita-jitar da masu kin kasar Sin na kasashen yammacin duniya suka yada ta hanyar ganin hakikanin yanayin yankin Tibet

2021-05-22 18:23:32 CRI

Gwamnatin kasar Sin ta gabatar da takardar bayani game da ‘yantar da yankin Tibet cikin lumana da samun ci gaba da wadata, inda aka yi bayani game da nasarorin da aka samu a yankin Tibet a cikin shekaru 70 da ‘yantar da shi cikin lumana. Akwai tarihi da kididdiga a cikin takardar, wadanda suka musunta jita-jitar da masu kin kasar Sin na kasashen yammacin duniya suka yada game da batun hakkin dan Adam na yankin Tibet, wato ta wannan takarda, duniya za ta gano hakikanin yanayin yankin Tibet.

Yawan GDPn yankin Tibet a shekarar 1951 ya kai Yuan miliyan 129 kadai, amma adadin a shekarar 2020 ya zarce Yuan biliyan 190. Yawan kudin shigar kowane mutumin yankin a shekarar 2020 ya karu tare da ninkawa sau biyu bisa na shekarar 2010.

A sa’i daya kuma, an kiyaye al’adun gargajiya da tabbatar da bin addini cikin ‘yanci a yankin. A halin yanzu, akwai wuraren ayyukan ibada na addinin Buddha na salon Tibet fiye da 1700 a yankin, kuma yawan masu bin addinin ya kai kimanin dubu 46.

Bisa wannan hakikanin yanayin yankin, za a gano cewa jita-jitar da masu kin kasar Sin na kasashen yammacin duniya suka yada kan batun hakkin dan Adam na yankin Tibet ba su da tushe. A hakika dai, batun yankin Tibet ba batun kabilanci ko addini ba ne, kana ba batun hakkin dan Adam ba ne, batu ne da ke shafar ikon mulkin kan kasar Sin da cikakken yankin kasar. An shafe lokaci mai tsawo, masu kin kasar Sin na kasashen yammacin duniya suna ta tsoma baki kan harkokin yankin Tibet, da yunkurin kawo illa ga zaman lafiyar al’ummar yankin. Burinsu shi ne maida batun yankin Tibet a matsayin batun hana ci gaban kasar Sin, inda suke amfani da batun hakkin dan Adam da batun addini don cimma wannan buri.

Yanzu an samu babban sauyi a yankin Tibet, masu kin kasar Sin ba su da damar tada rikici a yankin. Yunkurinsu na hana ci gaban kasar Sin ta hanyar fakewa da batun hakkin dan Adam, ba zai yi nasara ba. (Zainab)