logo

HAUSA

Majalisar gudanawa ta kasar Sin ta ba da takardar bayani kan ’yantar da yankin Tibet cikin lumana

2021-05-21 13:53:18 CRI

Yau Juma’a, majalisar gudanawa ta kasar Sin ta ba da takardar bayani kan ’yantar da yankin Tibet cikin lumana.

Bayanin ya nuna cewa, a ranar 23 ga watan Mayun shekarar 1951, gwamnatin kolin kasar Sin da gwamnatin yankin Tibet, sun kulla yarjejeniyar ’yantar da yankin Tibet cikin lumana, lokacin da aka sanar da ’yantar da yankin Tibet cikin lumana.
Bayanin ya ce, al’ummun yankin sun yi kwaskwarimar dimokuradiyya, karkashin jagorancin JKS, sun murkushe tsarin bayi manoma, da ’yantar da dubun dubantar bayi manoma, wadanda suka zama masu ’yancin kai, matakin da ya tabbatar da muradu masu tushe na al’ummu daban-daban, da kyautata zaman rayuwar jama’a.
Ban da wannan kuma, bayanin ya ce, yayin da ake shiga sabon karni, yankin na samun ci gaba mai armashi wajen yakar kangin talauci, abin da ya taimakawa yankin, wajen tabbatar da al’umma, da bunkasuwar tattalin arziki, da al’adu da kuma muhalli. (Amina Xu)