logo

HAUSA

Bikin tallata al’adun kasar Sin a makarantun Najeriya na bunkasa musaya tsakanin kasashen biyu

2021-05-21 14:18:55 CRI

Bikin tallata al’adun kasar Sin a makarantun Najeriya na bunkasa musaya tsakanin kasashen biyu_fororder_11

A kwanan nan ne aka yi gasar kade-kade da raye-raye mai taken “tallata al’adun kasar Sin a makarantu” a cibiyar al’adun kasar Sin dake Abuja, fadar mulkin tarayyar Najeriya, inda daliban makarantu 12 suka gabatar da kade-kade da raye-rayen kasashen biyu masu kayatarwa, a wani kokari na bunkasa musaya tsakanin al’adun su.

Domin karfafa hadin-gwiwar Sin da Najeriya a fannin al’adu, tun daga shekara ta 2013, ofishin jakadancin Sin dake Najeriya, da kuma hukumar kula da ilimin sakandare reshen babban birnin tarayyar kasar Abuja, su kan shirya gasar kade-kade da raye-raye mai taken “tallata al’adun kasar Sin a makarantu” a kowace shekara, domin kafa wani dandali ga daliban makarantu 12 dake Abuja gami da wuraren dake kewayensa da aka kafa “Chinese Corners”, don su nuna nasarorin da suka samu wajen karatun al’adun kasar Sin.

A nata bangaren, shugabar hukumar kula da ilimin sakandare reshen babban birnin tarayyar kasar Abuja Hajiya Fatima Gambo Babba ta bayyana cewa:

“Daliban makarantun mu suna sa ran halartar gasar a bana, al’amarin da zai ba mu damar kara fahimtar al’adun kasar Sin. Kana bisa ga wannan dama, muna taya kasar Sin murnar cika shekaru 100 da kafa jam’iyyar kwaminis, gami da cika shekaru 50 da kulla dangantakar diflomasiyya tsakanin Najeriya da Sin. Wannan hadin-gwiwa na cin moriyar juna ne, kuma dukkan mu muna sa ran kara samun makoma mai haske.”

Bikin tallata al’adun kasar Sin a makarantun Najeriya na bunkasa musaya tsakanin kasashen biyu_fororder_22

Shi ma a nasa bangaren, jami’i mai kula da harkokin al’adu na ofishin jakadancin Sin dake Najeriya, wanda kuma shi ne babban darektan cibiyar al’adun kasar Sin dake Abuja, Li Xuda, ya ce daliban makarantun da aka kafa “Chinese Corners” dake Abuja da sauran wurare sun koyi abubuwa da dama dangane da al’adun kasar Sin, inda ya ce:

“A ‘Chinese Corners’, daliban sun koyi al’adu da raye-raye da wasannin Kungfu da fasahar rubuce-rubucen gargajiya na kasar Sin, inda suka shaida nasarorin da aka samu wajen raya zumunta tsakanin Sin da Najeriya. A gasar da aka yi ta kowace shekara, a kan zabi dalibai uku da suka yi fice, wadanda za su samu damar shaida kwarewarsu a wasu ayyukan nuna al’adun kasar Sin, al’amarin da ya taimaka sosai ga al’ummar Najeriya musamman dalibai matasa wajen kara fahimtar kasar Sin, da yaukaka dankon zumunci tsakanin kasashen biyu.”

Wang Xiaojia, ‘yar kasar Sin ce daya kacal dake koyarwa a cikin makarantun 12 dake Abuja da ma wuraren dake kewayensa da aka kafa “Chinese Corners”. Tun daga shekara ta 2019, Wang ta fara koyar da harshen Sinanci gami da al’adun kasar a wata makarantar kasa da kasa dake garin Suleja na jihar Neja. Malama Wang ta bayyana cewa:

“Dalibai na suna son wake-wake da raye-raye, ina ganin ta hanyar halartar wadannan ayyukan al’adu, za su kara sha’awar al’adun kasar Sin, kuma watakila za su ci gaba da koyon yaren Sinanci idan sun girma. A makarantarmu, dalibai su kan ce min ‘Ni Hao! Ni Hao!’ wato barka a kowace rana. Kuma dalibai suna matukar sha’awar koyon yaren Sinanci a darasina.”

Bikin tallata al’adun kasar Sin a makarantun Najeriya na bunkasa musaya tsakanin kasashen biyu_fororder_33

Aminu Jemiu wanda ya taba zama da karatu a birnin Beijing na tsawon shekaru uku, ya iya yaren Sinanci gami da gabatar da al’adun Sin sosai. Aminu ya bayyana cewa:

“Akwai kyakkyawar dangantaka tsakanin Najeriya da Sin! Wasannin da aka gabatar yau sun kayatar da mu sosai, gaskiya mun jin dadi. A ganina Sin babbar kasa ce mai yawan al’umma kuma mai tsabta, ina son al’ummar Sin gami da abincin kasar. Ina mai fatan kasashen biyu za su karfafa hadin-gwiwarsu, kuma za mu samu makoma mai kyau a nan gaba.”

Ban da wake-wake da raye-rayen da suka shafi kasar Sin, a wajen gasar da aka yi, daliban makarantun 12 sun kuma yi gasar wake-wake gami da raye-rayen zamani da na gargajiya na Najeriya, abun da ya shaida musayar al’adu tsakanin kasashen biyu. (Murtala Zhang)