logo

HAUSA

Sin na goyon bayan gaggauta samar da karin rigakafin COVID-19 ga nahiyar Afirka

2021-05-20 14:55:59 CRI

Sin na goyon bayan gaggauta samar da karin rigakafin COVID-19 ga nahiyar Afirka_fororder_0520-1

Sin na goyon bayan gaggauta samar da karin rigakafin COVID-19 ga nahiyar Afirka_fororder_0520-2

A baya bayan nan, sassan masu ruwa da tsaki na matsa kaimin yin kiraye kiraye, game da bukatar samarwa kasashen Afirka karin alluran rigakafin cutar COVID-19, wadda ke ci gaba da yaduwa a sassa daban daban na duniya.

Ko shakka babu, kasar Sin tana sahun gaba wajen yin wannan kira, inda a kwanan nan aka jiyo dan majalissar gudanarwar kasar, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, na jaddada kira ga kasashen duniya kan batun. Yana mai cewa Afirka na bukatar tallafin kayan yaki da annobar, da rigakafi da magunguna, da fasahohi da kudade, da musayar fasaha, da hadin gwiwar samar da rigakafi, ta yadda hakan zai tabbatar da cewa, kasashen nahiyar sun samu isassun rigakafin cutar cikin sauki.

Su ma sassan masu ruwa da tsaki na nahiyar ta Afirka, na bayyana damuwa game da karancin samun rigakafin cutar COVID-19, lamarin da ake dangantawa da boye alluran da wasu kasashe masu wadata ke yi.

Yanzu haka dai a wasu sassan fadin duniya, an kai ga yiwa mutum kusan 15 cikin duk mutane 1,00 rigakafin cutar, sai dai kuma a yankin kudu da Hamadar Sahara, adadin bai wuce mutum 0.8 cikin duk mutane 1,00 ba. Ko shakka babu, hakan na nuni ga wagegen gibin da ake da shi a fannin baiwa daukacin al’ummun duniya rigakafin na COVID-19 bisa daidaito.

Masharhanta da dama na ganin shirin samar da rigakafi ga kasashe masu rauni na COVAX wanda MDD ke jagoranta, zai magance rashin daidaiton gudanar da rigakafin a sassan duniya, to sai dai kuma, bayan fara aiwatar da shi a watan Fabarairu, shirin ya gaza cimma cikakkiyar nasara a kasashen nahiyar da dama. Ko da yake wasu daga kasashen na Afirka sun karbi kyautar rigakafin daga kasashe irin su Sin da Rasha, da sauran su.

Masana dai sun yi amannar cewa, ba wata dabara mafi dacewa da za a bi, wajen shawo kan yaduwar wannan annoba a duniya baki daya, wadda ta wuce yiwa kaso mai yawa na al’ummun duniya rigakafin cutar ta COVID-19.

Don haka dai, kiraye-kiraye daga kasar Sin, da masu ruwa da tsaki daga Afirka, da kuma hukumar lafiya ta duniya WHO, game da wajibcin samar da rigakafin wannan cuta ga Afirka, mataki ne mai fa’idar gaske. Domin kuwa wadatar rigakafin a kasashen Afirka, da sauran sassan duniya baki daya, tamkar salon maganar nan ne na “Yiwa wani yiwa kai!” (Saminu Hassan)