logo

HAUSA

An yi taron karawa juna sani kan cika shekaru 70 da samun ‘yancin kan jihar Tibet

2021-05-20 13:39:51 CRI

An yi taron karawa juna sani kan cika shekaru 70 da samun ‘yancin kan jihar Tibet_fororder_hoto

A jiya Laraba ne aka gudanar da taron karawa juna sani, game da cika shekaru 70 da samun ‘yancin kan jihar Tibet ta kasar Sin, a cibiyar nazarin ilmin jihar Tibet ta kasar Sin.

A yayin taron, mataimakin shugaban kungiyar kiyaye da raya al’adun jihar Tibet ta kasar Sin, Si Ta, ya bayyana cewa, cikin shekaru 70 da suka gabata, na samun ‘yancin kan yankin, al’ummun jihar na cikin zaman lafiya, kuma tsarin zaman takewar al’umma na jihar ya kyautata sosai, lamarin da ya taimakawa al’ummomin jihar a fannin kyautata rayuwarsu, da raya al’adunsu. Kana, ana kiyaye ‘yancin bin addinai na al’ummomin jihar kamar yadda ake fata, da kuma kare muhallin jihar yadda ya kamata.

Yanzu haka dai, jihar Tibet ta kasance daya daga cikin wurare masu kyakkyawan muhalli.

Kwararen kasar Amurka Laurence Brahm ya ce, ana kiyaye al’adu na kabilu daban daban a jihar Tibet yadda ya kamata, kuma al’ummomin jihar suna da hakuri da mutunta juna, lamarin da ya tabbatar da dauwamammen ci gaban al’adunsu.

Kaza lika, masanin kasar Pakistan Ejaz Akram ya ce, kasar Sin ta yi kokari matuka, wajen kawar da talauci a cikin gida, ta kuma cimma babbar nasara. Ya ce yanzu haka shawarar “Ziri daya da hanya daya”, tana taimakawa kasashen da abin ya shafa, wajen neman ci gaba cikin lumana da kuma kawar da talauci.

Wasu rahotanni sun nuna cewa, kungiyar nazarin hakkin dan Adam ta kasar Sin, da kungiyar kiyaye da kare al’adun jihar Tibet, da kuma cibiyar nazarin ilmin jihar Tibet ta kasar Sin, sun gudanar da taro cikin hadin gwiwa. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)