logo

HAUSA

Kwamitin sulhun MDD ya zartas da sanarwar shugaba dangane da batun farfadowar Afirka bayan annobar Covid-19

2021-05-20 13:46:21 CRI

Kwamitin sulhun MDD ya zartas da sanarwar shugaba dangane da batun farfadowar Afirka bayan annobar Covid-19_fororder_4a36acaf2edda3ccf2244013933ab207203f921f

A jiya Laraba, a matsayinta na kasar da ke shugabantar kwamitin sulhu a halin yanzu, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya shugabanci babban taron kwamitin sulhun MDD, taron da ke da jigon “zaman lafiya da tsaron Afirka, farfadowa da Afirka bayan annobar Covid-19 da kawar da tushen rikici”, inda kuma mambobin kwamitin suka zartas da sanarwar shugaba, wadda kasar Sin ta tsara. Wakiliyarmu Lubabatu na tare da karin haske.

Sanarwar shugaban ya jaddada cewa, yadda annobar Covid-19 ke illata fannonin tattalin arziki, da siyasa da tsaro da jin kai a kasashen Afirka, na matukar jawo hankalin kwamitin sulhu, wadda kuma ya kara tsananta yanayin rikici a nahiyar. Kamata ya yi kasa da kasa su karfafa hadin kai, kuma MDD ta taka rawar da ta wajaba, don tinkarar matsalar yadda ya kamata.

Baya ga haka, ya kamata a kara samar da tallafi ga kasashen Afirka, musamman ma kasashen da rikice-rikice suka fi shafa. Kana a kara samar da gudummawar kayayyakin jinya da na gwajin cutar COVID-19 da ma rigakafinta, don tabbatar da kowa ya iya samun jinya da rigakafi bisa adalci.

Yanzu haka ana tattauna batun janye kariyar hakkin mallakar ilmin harhada rigakafin cutar Covid-19, a karkashin tsarin kungiyar cinikayya ta duniya (WTO). A ganin kwamitin sulhun, dole ne a kara samar da sinadarai na hada rigakafi, sa’an nan, a yi musayar fasahohi, da hakkin mallakar ilmin harhada rigakafin, bisa ga amincewar bangarori masu ruwa da tsaki.

Sanarwar ta yi nuni da cewa, kawar da tushen rikici a Afirka na da muhimmanci sosai. Don haka ya kamata a dauki matakai daga bangarori daban daban, kuma a hada karfi da karfe, don sa kaimin samar da dauwamammen ci gaban tattalin arziki da saukaka fatara, tare da aza harsashi mai inganci, na tabbatar da zaman lafiya.

Har ila yau, a inganta harkokin ilmantarwa, da kiwon lafiya, da walwalar al’umma, don kawar da tushen aukuwar rikici, tare da hana bazuwar ta’addanci da tsattsauran ra’ayi a Afirka. Baya ga haka, a karfafa gwiwar MDD, ta yadda za a inganta hadin gwiwa da kungiyoyin Afirka, a kokarin farfadowa da kasashen nahiyar bayan annobar Covid-19.

Sanarwar ta kara da cewa, ya kamata a bi hanyar yin shawarwari, don daidaita matsalolin dake fuskanta a siyasance, a kuma sa kaimi ga bangarorin dake arangama da juna, ta yadda za su daina daukar matakan gaba da juna, don cimma burin dakatar da karar bindiga. Ya kamata MDD ta taimakawa kasashen Afirka, wajen cimma burin sulhunta tsakanin kabilu daban daban.

Har wa yau, sanarwar ta ce ayyukan kiyaye zaman lafiya da MDD ke aiwatarwa, na taka muhimiyyar rawa, wajen kiyaye zaman lafiya da tsaro a Afirka, don haka ya kamata a aiwatar da su ba tare da tsayawa ba, don samar da yanayin da ya dace, na farfado da tattalin arzikin kasashen da rikici ya shafa. Sa’an nan, ya kamata a kiyaye tsaron ma’aikata kiyaye zaman lafiya.

Sanarwar ta kuma yi nuni da cewa, bunkasuwar zamantakewar al’umma, da tattalin arziki, na da matukar muhimmanci wajen kiyaye dauwamammen zaman lafiya a Afirka. Kuma ya kamata a tabbatar da ajandar tarayyar Afirka nan da shekarar 2063, da ma muradun MDD na samun dauwamammen ci gaba nan da shekarar 2030, kuma ta hanyoyin gina manyan ababen more rayuwa a tsakanin kasashe da shiyyoyi daban daban, da raya masana’antu, da saukaka fatara, da samar da guraben aikin yi, da bunkasa ayyukan gona na zamani, a tabbatar da bunkasuwar tattalin arzikin kasashen Afirka da dunkulewarsu baki daya, ta yadda za a kiyaye dauwamammen zaman lafiya a nahiyar.

Daga karshe, ya kamata a mara wa kasashen Afirka baya, wajen tsara manufofi na tinkarar sauyin yanayi, da sauyin muhalli, da bala’u daga indallahi, kuma a tabbatar da hakkin mata na sa hannu, a tsara manufofi da suka shafi kiyaye zaman lafiya da tsaro da bunkasuwa.  (Lubabatu)