logo

HAUSA

Nasarorin kasar Sin a fannin binciken sararin Samaniya

2021-05-19 09:13:11 CRI

A kwanakin baya ne, na’urar binciken duniyar Mars da ake kira Tianwen-1 ta yi nasarar sauka a doron duniyar Mars, al’amarin da ya shaida cewa, a karon farko na’urar binciken duniyar Mars ta kasar Sin, ta sauka cikin nasara. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taya daukacin ma’aikatan dake kula da wannan aiki murna tare da jinjina musu.

Nasarorin kasar Sin a fannin binciken sararin Samaniya_fororder_210519世界21018-hoto1

A sakonsa, shugaba Xi ya nuna cewa, saukar na’urar Tianwen-1 a duniyar Mars, muhimmin ci gaba ne da kasar Sin ta samu a fannin binciken sararin samaniya. Wato a karon farko, kasar Sin ta fara gudanar da bincike a duniyar Mars, lamarin dake da muhimmanci ga bangaren binciken sararin samaniya na kasar.

Tun a ranar a 23 ga watan Yulin bara ne, aka yi amfani da rokar LongMarch-5 wajen harba na’urar Tianwen-1 a birnin Wenchang na lardin Hainan dake kudancin kasar Sin, kana ta yi nasarar shiga falakin duniyar Mars a ranar 10 ga watan Fabrairun bana. Sa’annan tun daga ranar 24 ga watan Fabrairun, ta soma kewaye duniyar Mars don gudanar da bincike har na tsawon wata uku, abun da ya aza tubali mai inganci ga sauka a doron duniyar.

Nasarorin kasar Sin a fannin binciken sararin Samaniya_fororder_210519世界21018-hoto3

Cimma nasarar saukar na’urar bincike ta Tianwen-1 a duniyar Mars, ta sa Sin ta zama kasa ta biyu a duniya, da na’urar bincikenta ta sauka a duniyar ta Mars ba tare da wata matsala ba

Wannan shi ne karo na farko a duniya da aka samu nasarar tafiya da kuma sauka a duniyar Mars a lokacin harba na’ura a karo guda, kuma hakan ya baiwa kasar Sin damar zama a sahun gaba a duniya fannin binciken duniyar Mars.

Kafin haka, kasar Sin ta yi nasarar debo wasu samfura daga bangaren duniyar wata mai nisa, ta kuma yi nasarar harba wani bangare na dakin binciken sararin samaniya nata na kanta. Wannan yana kara nuna irin ci gaban da kasar Sin ta ke samu a aikin binciken sararin samaniya, sakamakon da ta ce zai amfani duniya baki daya. (Saminu, Ibrahim /Sanusi Chen)