logo

HAUSA

Sin ta shaidawa duniya cewa, samun bunkasuwa hanya ce mafi muhimmanci ta kawar da talauci

2021-05-19 15:59:43 CRI

Jaridar “Leadership A Yau” ta Najeriya ta ba da labari a kwanan baya cewa, kimiyya na baiwa kauyukan kasar Sin karfi, wajen ci gaba da samun bunkasuwa bayan sun fita daga talauci.

A hakika, dogara da kimiyya da fasaha da bunkasa aikin noma mai kiyaye muhalli, hanya ce mafi dacewa wajen kara kudin shigar manoma. Masanin kimiyyar aikin gona na kasar Najeriya Ibrahim Argongu, ya ganewa idanunsa yadda kauyukan kasar Sin suka fita daga kangin talauci bisa dogaro da kimiyya.

Ibrahim yana aiki ne a wani kamfanin gandun noma mallakar Sinawa a Najeriya, wanda ya fitar da wani shirin da zai iya taimaka ga kara samar da shinkafa bisa irin yanayin noma da ake ciki a wurin da ma yin amfani da fasahohin kasar Sin. Har mazauna wuri suna ta zuwa gandun don sayen ire-iren shinkafa da koyon ilmi da kimiyya, saboda ba ma kawai wadannan dabaru sun taimakawa mazauna wuri wajen samun isashen hatsi ba ne, har ma suna taimaka musu samun karin kudin shiga.

A shekarar 2015, Ibrahim Argongu ya samun damar zuwa birnin Changsha na kasar Sin don koyon fasahar renon irin shinfaka mai inganci. Ya ce, a lokacin da yake a kasar Sin na tsawon watanni uku, ya ganewa idanunsa bunkasuwar kimiyya da fasahar kasar Sin, a fannoni daban-daban musamman ma kimiyyar aikin noma ta zamani.

Ziyarar kasar Sin ta taimakawa Ibrahim Argongu, wajen fahimtar dalilin da ya fitar da manoman kasar Sin daga kangin talauci. A ganinsa ya kamata Najeriya ta koyi dabarun kasar Sin, na warware matsalar talauci tsakanin manoma. Ya ce, Sin ta cimma nasara kan manufofin da ta dauka kan sha’anin noma, da taimakawa manoma, da raya kauyuka, manufofin da ya kamata su zama abin koyi ga sauran kasashe.

Manoma suna da yawa a kasar Sin, kuma da yawa daga cikinsu sun kasance cikin kangin talauci, don haka abu ne mai wuya a kawar da talauci. Duk da haka, a shekarar 2020, Sin ta cimma nasarar kawar da talauci, inda mutane kimanin miliyan 100 suka fita daga kangin talauci, kuma dukkanin gundumomi dake fama da talauci sun samu kubuta. Hakan ya sa Sin ta kawar da talauci baki daya a duk fadin kasar.

Bayan da Sin ta cimma nasarar dakile kangin talauci, kasar ba ta tsaya ba, a maimakon haka, tana ci gaba da kokarin raya kauyuka. Ban da wannan kuma, don inganta nasarorin da ta cimma wajen saukaka fatara, a wannan shekara, gwamnatin Sin ta samar da tallafin kudi har Yuan biliyan 15.61, don taimakawa wadanda suka fito daga kangin talauci, ta yadda ba za su sake fadawa talauci ba, da kuma tallafa musu wajen kyautata zaman rayuwarsu.

Yaki da talauci aiki ne a gaban Bil Adama baki daya, Sin ta cimma nasararsa shekaru 10 kafin an kammala wa’adin burin samun bunkasuwa mai dorewa na MDD nan da shekarar 2030, inda kasar ta zama jagora mai ba da taimako, kuma mai sa kaimi ga wannan sha’ani, abin da ya bayyana ingancin manufofin da Sin take dauka na daidaita harkokinta.

Kauyukan Sin sun fita daga talauci, kuma za su samu wadata nan gaba. Duk wadannan matakai sun bayyana wa duniya baki daya cewa, hanyar da ta fi dacewa wajen kawar da talauci ita ce samun bunkasuwa. (Amina Xu)