logo

HAUSA

Duniya Za Ta Amfana Da Nasarar Kasar Sin A Fannin Binciken Sararin Samaniya

2021-05-19 16:07:24 CRI

Duniya Za Ta Amfana Da Nasarar Kasar Sin A Fannin Binciken Sararin Samaniya_fororder_0519-1

A kwanakin baya ne, na’urar binciken duniyar Mars ta kasar Sin da ake kira Tianwen-1 ta yi nasarar sauka a doron duniyar Mars, al’amarin da ya shaida cewa, a karon farko na’urar binciken duniyar Mars ta kasar Sin, ta sauka cikin nasara.

Jim kadan da samun wannan nasara wadda ta janyo hankalin kasashen duniya matuka, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taya daukacin ma’aikatan dake kula da wannan aiki murna tare da jinjina musu.

Yana mai cewa, saukar na’urar Tianwen-1 a duniyar Mars, muhimmin ci gaba ne da kasar Sin ta samu a fannin binciken sararin samaniya. Kuma karon farko, da kasar Sin ta fara gudanar da bincike a duniyar Mars, lamarin dake da muhimmanci ga bangaren binciken sararin samaniya na kasar.

Kafin haka, kasar Sin ta yi nasarar debo wasu samfura daga bangaren duniyar wata mai nisa, ta kuma yi nasarar harba wani bangare na dakin binciken sararin samaniya nata na kanta. Wannan yana kara nuna irin ci gaban da kasar Sin take samu a aikin binciken sararin samaniya, sakamakon da ta ce zai amfani duniya baki daya. Ta kuma nemi kasashen duniya dake da sha’awar bunkasa wannan fanni, da su zo a hada hannu, ta yadda za a cimma nasara da moriya tare a fannin binciken sararin samaniya cikin lumana

Bayanai na nuna cewa, tun a ranar 19 ga watan Yulin shekarar 1964 ne, kasar Sin ta fara daukar matakai a hukumance game da harba roka na gwaji dauke da bera zuwa sararin samaniya, da kuma lokuta daban-daban, da take harba na’urori da kumbon binciken sararin samaniya kala-kala, kamar Chang’e-1 zuwa 5 da Tiangong-1 da tsarin taurarin dan-Adam na ba da jagorancin taswira na Beidou da sauransu, abin da ke nuna tarin nasarorin da kasar ta cimma a aikin binciken sararin samaniya

Saukar na’urar bincike ta Tianwen-1 a duniyar Mars cikin nasara, ta sa kasar Sin ta zama kasa ta biyu a duniya, da na’urar bincikenta ta sauka a duniyar ta Mars ba tare da wata matsala ba. Wannan wata kyakkyawar alama ce dake nuna nasarar kasar a fannin binciken sararin samaniya.

Kasar Sin ta sha nanata cewa, za ta martaba tunanin amfanawa dukkan bil- Adam, da ci gaba da sa kaimi ga yin hadin gwiwa a tsakaninta da sauran kasashen duniya, da kara samar da gudummawa a aikin binciken sararin samaniya da samun ci gaba cikin lumana. Kyakkyawar Jumma’a tun daga Laraba ake gane ta. (Ibrahim Yaya)