Aminu Inuwa Darma: Ya kamata matasan Najeriya su tashi tsaye don gina kasa
2021-05-18 14:31:20 CRI
Aminu Inuwa Darma, dan asalin karamar hukumar Kumbotso dake jihar Kanon Najeriya ne, wanda a yanzu haka yake karatun neman digiri na uku a kwalejin nazarin ilimin noma ta kasar Sin dake Beijing.
A yayin zantawar sa da Murtala Zhang, Aminu Darma ya bayyana ra’ayinsa kan bambancin tsarin ilimin dake kasancewa tsakanin kasar Sin da kasar Najeriya.
Ya kuma bayyana yadda kasar Sin ta samu babban ci gaba a fannin dakile cutar mashako ta COVID-19, musamman karkashin jagorancin jam’iyyar kwaminis ta kasar, inda ya ce jam’iyya ce mai lura da moriyar al’umma gami da cusawa al’umma akidar kishin kasa.
A karshe, malam Aminu Darma ya yi kira ga matasan Najeriya da ma duk Afirka baki daya, su tsahi tsaye don nuna jajircewa wajen gina kasashen su. (Murtala Zhang)