logo

HAUSA

Ci Gaba Da Bude Wuta Tsakanin Isra’ila Da Hamas Ba Zai Taba Haifar Da Da Mai Ido Ba

2021-05-18 15:15:40 CRI

Ci Gaba Da Bude Wuta Tsakanin Isra’ila Da Hamas Ba Zai Taba Haifar Da Da Mai Ido Ba_fororder_0518-1

Ci Gaba Da Bude Wuta Tsakanin Isra’ila Da Hamas Ba Zai Taba Haifar Da Da Mai Ido Ba_fororder_0518-2

Zuwa yanzu, an shafe kwanaki 9 ana rikici tsakanin Isra’ila da kungiyar Hamas ta Falasdinu mai rike da iko da zirin Gaza, inda alkaluma suka nuna cewa, kawo yanzu, rikicin wanda shi ne mafi muni tsakanin makwabtan biyu tun bayan shekarar 2014, ya yi sanadin rayukan Falasdinawa 204, ciki har da yara 59 da Isra’ilawa 10, ciki har da yaro dan shekaru 5 da soja guda.

Wannan rikici da dukkan bangarori ke kokarin nuna karfi, ba zai taba kai wa ga cimma sulhu ko biyan bukatar kowanne bangare ba, sai ma dai kara illata dangantakarsu da jefa rayukan fararen hula da ba su ji ba, ba su gani ba cikin garari.

A matsayinta na shugabar kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na watan Mayu, kasar Sin tare da kasashen Norway da Tunisia, sun ingiza kira wani taron gaggawa kan batun a ranar Lahadin da ta gabata, duk da cewa suna so kiran taron tun da wuri a ranar Juma’a, amma sai Amurka ta hau kujerar naki.

Daga bisani dai an gudanar da taron a ranar Lahadi inda mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi ya gabatar da wasu shawarwari 4.

Da farko, ya bada shawarar dakatar da kai hare hare nan take. Har kullum, kasar Sin ta kasance mai nacewa ga tattaunawa da sulhu maimakon nuna karfi. Idan har aka gaza kai zuciya nesa aka ci gaba da kai hare-hare, tabbas asarar da hakan za ta haifar na da dimbin yawa, kana lamarin zai zarce tsakanin Falasdinu da Isra’ila ya kai ga sauran kasashe kawayensu, al’amarin da zai kawo rabuwar kawuna da karin tashin hankali a duniya, wanda ba a bukatarsa ko kadan. Dama can yankin gabas ta tsakiya na cikin wani yanayi, don haka, ci gaba da rikicin ka iya kara kai wa ga tabarbarewar al’amura.

Shawara ta biyu ita ce, bukatar kai agajin jin kai. Lallai ya zama tilas kasa da kasa su hada hannu wajen kai wa al’umma dauki. Bisa rahotannin da ake samu, mutane a yankin Zirin Gaza na cikin tsananin bukatar daukin abinci, ruwa, matsauguni har ma da asibitoci da sauransu. Don haka ya kamata a gaggauta kai musu dauki da dukkan sauran mutanen dake bukatar agaji domin kaucewa ta’azzarar lamarin.

Shawara ta uku ita ce: wajibi ne kasashen duniya su taimaka. Wannan lokaci ne na ajiye banbancin ra’ayi da siyasa da akida, a hada hannu wajen lalubo hanyoyin yayyafawa rikicin Isra’ila da Falasdinu ruwa. Farkon rikici aka sani, ba a san karshensa. Abun takaici ne yadda kwanaki bayan dukkan mambobin kwamitin sulhu sun amince da kudurin inganta huldar kasa da kasa, sai Amurka ta toshe gudanar da taron kan rikicin a ranar Juma’a. A matsayinta na babbar kasa ta hau kujerar naki har sau uku, lamarin da ya hana kwamitin sulhun fitar da wata sanarwa guda dangane da rikicin, haka kuma sai da ta sha matsi sannan ta goyi bayan tsagaita bude wuta. kamata ya yi a rika jin amon manyan kasashe da murya guda a irin wannan lokaci. Kamata ya yi kasashe irin Amurka su yi la’akari da abun da rabuwar kai zai haifar ga makomar bil adama. Hadin kai da ingantacciyar hulda tsakanin kasa da kasa, hanya ce mafi dacewa ta wanzar da zaman lafiya a duniya da shawo kan kalubale daban daban da ake fuskanta, da gina al’umma mai makoma ta bai daya ga bil adama.

A cewar Wang Yi, shawara ta hudu ita ce, kafa ’yantattun kasashe biyu. Kamar yadda ministan na kasar Sin ya bayyana, kafa kasashe biyu shi ne tubalin warware wannan rikici da yaki ci yaki cinyewa tsakanin Isra’ila da Falasdinu. Haka za lika shi ne zai tabbatar da yancin kowanne bangare. Lallai idan ana son ganin zaman lafiya a yankin, ya kamata a tabbatar da warware tushen rikicin bangarorin biyu dake zaman ‘yan uwa kuma makwabta.  (Faeza Mustapha)