logo

HAUSA

Kwarewar Kelbinur Kurban ‘yar shekaru 21 a fannin kasuwanci

2021-05-17 13:48:19 cri

Kelbinur Kurban, wata yariniya daga Turpan na jihar Xinjiang ta kasar Sin, tana da shekaru 21. Yanzu haka ta kammala karatunta a harkar kasuwanci ta yanar gizo a Kwalejin Koyon Fasaha ta Xinjiang a shekarar 2020, a watan Yulin shekarar kuma, ta shiga kamfanin kasuwanci wanda mahaifinta ya kafa don yin gwajin aiki, daga baya kuma ta dauki nauyin kasuwancin mahaifinta a watan Nuwamba, hakan ya sa ta kasance shugabar wannan kamfanin ... Ko irin wannan nauyin dake bisa wuyanta ya kawo mata matsin ko a’a? To, masu sauraro, a cikin shirinmu na yau za mu kawo muku bayani ne game da labarin wannan matashiya mai suna Kelbinur Kurban, yar kabilar Uygur ta jihar Xinjiang.

Da karfe 10 na safe, sai Kelbinur Kurban ta fara aikinta kamar yadda ta saba, kamar su bincika kaya tare da mahaifinta Kurban Mettohti, da duba tallace-tallace da kamfanin ya yi a yanar gizo, da tattaunawa da ma'aikata a sassan masana'antar, da kuma duba ci gaban fitar da kayayyaki da ingancin kayayyaki, baya ga haka kuma za ta share fagen maraba da rukunonin masu yawon bude ido daga sauran wurare ... A gare ta, duk abin da take yi yanzu suna taimaka mata wajen kara koyon abubuwa da kuma girma a fannin kasuwanci.

Kelbinur Kurban tana matukar yaba wa mahaifinta. Har yanzu tana iya tuna kwarewar mahaifinta a fagen gudanar da kasuwanci daga sayar da katifu domin ciyar iyalinsu a yankin Hotan zuwa bude shagon kafet na sama da murabba'in mita 560 a Turpan.

Kwarewar Kelbinur Kurban ‘yar shekaru 21 a fannin kasuwanci_fororder___172.100.100.3_temp_9500049_1_9500049_1_1_6b730f62-e287-4ec9-ba89-6bf5345485c6

Tana kuma godiya ga gwamnatin wurin da ta samar da sauki a fannonin zabar wurin kafa kamfani da rajista ga mahaifinta yayin da ya soma kafa masana'antar saka kafet da hannu a ‘yan shekarun da suka gabata, kana bisa tsarin samar da kudin tallafi ga matsakaita da kananan masana’antu ne, gwmnatin ta samar da kudi ga mahaifinta don warware matsalar rashin kudin soma aiki.

Wannan kuma shi ne dalilin da ya sa Kelbinur Kurban ta yi kokari sosai bayan ta karbi kamfanin.

A halin yanzu, kamfanin da take gudanarwa wanda ke da murabba'in mita 5,000 yana samun kudin shiga Yuan miliyan 15 kwatankwacin dalar Amurka kusan 2.5 a kowace shekara. Babban kasuwancin kamfanin shi ne zane, samarwa, da sayar da kayan saka masu sigar musamman na kananan kabilun dake jihar Xinjiang, ciki har da yadin Adelais da kafet.

Ba wai kawai tana son gudanar da kasuwancin da ta gada daga mahaifinta ba ne, har ma tana tunanin yadda za ta dogara da wannan masana'antar dinkin kafet da hannu don taimakawa mutane mafi yawa wajen samu aikin yi, kuma a lokaci guda a yada irin fasahar gargajiyar ta dinkin kafet da hannu.

Ko a fannin salo, ko zane ko kuma launi, kafet da aka saka da hannu irin na kabilar Uygur suna da halin musamman na kabilar. Kullum an san su da kayan aiki da fasaha masu kyau, da siffofi na musamman, da kwarewar masu saka, da launuka masu kyau. Hanyar sakan tana da fasaharta ta musamman, kuma adadin launi ko yawa ko karfin launika ko fasahar 3D ba sa zama cikas ga wannan wannan hanyar saka.

Kwarewar Kelbinur Kurban ‘yar shekaru 21 a fannin kasuwanci

Kelbinur Kurban ta bayyana cewa, suna yin kafet da aka yi da hannu a nan. Suna fatan yada irin fasahar yadda ya kamata. Kuma suna da matukar bukatu a kan aikin hannu. Bayan ma'aikata sun zo nan don aiki, za su samu horo na musamman daga wajen kwararru. A yanzu haka akwai ma'aikata 34, kashi daya bisa uku daga cikinsu nakasassu ne. Suna samar musu da aiki mai kyau a kusa da gida. A cewarta, kamfaninta ya riga ya kasance cibiyar horas da kayan masaku a Turpan, wanda ke iya samar da kafet da aka yi da hannu masu murabba'in mita 150 a kowace shekara.

Da tsakar rana, a zauren baje kolin na hawa na farko na kamfani, Kelbinur Kurban ta karbi wata kungiyar masu yawon bude ido, inda ta gabatar da zane-zane da halin musamman na kafet din ga baki, sannan kuma ta jagorance su ziyartar gidan ajiye kafet irin na gargajiya da ke hawa na biyu.

A cikin gidan kayan tarihin, Kelbinur Kurban ta gabatar da injunan saka kafet da hannu na gargajiyar jihar Xinjiang da kuma yadda suke samun ingantuwa da sabunta. Har ila yau, ita da kanta ta sarrafa wata na’ura tare da bayyana fsahar saka kafet da hannu. Wadannan labaru masu dadi da kuma tsohon tarihin kafet na jihar Xinjiang sun ta da sha'awar masu yawon bude ido sosai. Abin da yafi birgewa shi ne, a hawa na uku na ginin baje kolin, akwai kuma masaukin baki mai salon musamman na gargajiya.

A yayin da ake kokarin sayar da kafet, a waje guda kuma an gina gidan ajiye kayan tarihi da masaukin baki, don samun ci gaba ta hanyar raya sana’ar yawon shakatawa, wannan ra’ayi ya zo daga wajen Kelbinur Kurban. Ta bayyana cewa, a farko, ba ta ra’ayi kan bunkasa kasuwancin. Amma daga baya, sai ta yi tunanin gina gidan adana kayan tarihi. Hakan, za a iya hada da fitarwa da kayayyaki da sayarwa da kuma ziyara tare, ta yadda kasuwancinsu zai inganta sosai.

Yanzu ga alama, ra'ayoyinta na rashin tsayawa ga hanyoyin kasuwancin gargajiya suna amfani sosai. Wannan kuma ya sa iyalinta da ma’aikata sun kara amincewa da ita.

Kamar yadda Kelbinur Kurban ta fada, "A da, mu kan jira wasu su sayi kayayyakinmu. Tun lokacin da na karbi kamfanin, ina so in fitar da kayanmu waje, da kuma sanya mutane masu yawa su san kayanmu, wannan shi ne buri na."