logo

HAUSA

Yadda JKS Ke Kula Da Jama’ar Kasa Ya Ja Hankalin Masanan Kasa Da Kasa

2021-05-17 19:15:24 CRI

Yadda JKS Ke Kula Da Jama’ar Kasa Ya Ja Hankalin Masanan Kasa Da Kasa_fororder_0517-1

Ga dukkan masu bibiyar yadda tarihi da al’amurran kasar Sin ke wakana za a fahimci yadda manufofin mahukuntan kasar suka karkata wajen hidimtawa al’ummarsu tare da mayar da jama’ar kasar a gaban komai. Wannan jajircewar da jagororin kasar suka nuna shi ne ya kai ta ga matsayin ci gaba da ta samu a halin yanzu. Alal misali, a ranar 25 ga watan Fabrairun bana, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da cewa, kasar ta cimma nasarar kawar da talauci baki daya daga cikin gidanta. Batun da ya ja hankalin kafofin watsa labaru na kasa da kasa matuka, har ma wasu na gabatar da tambayar cewa shin ta yaya kasar Sin ta samu nasarar kawar da talauci, a matsayinta na wata kasa mai tasowa dake da yawan al’umma da ya kai biliyan 1 da miliyan 400?

Koda a kwanakin baya-bayan nan wani tsohon shugaban cibiyar nazarin zaman lafiya da daidaita rikice-rikice ta Nijeriya, Goseph Golwa, ya fidda sharhi mai taken “Yadda Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin take dukufa wajen kula da jama’ar kasa, ya sa kasar ta sami ci gaba na a zo a gani” wanda aka wallafa a jaridar BLUEPRINT ta Najeriya. Cikin sharhin ya bayyana cewa, a ko da yaushe, JKS tana maida aikin kyautata rayuwar al’umma a matsayin babban burinta, ta kuma cimma babbar nasara a wannan fanni. Ya ce a bana, ake cika shekaru 100 da kafuwar jam’iyyar, kuma tabbas kasar Sin za ta ba da karin gudummawa a fannin kare zaman lafiyar kasa da kasa, da inganta bunkasuwar kasashen duniya, da kuma kare tsarin kasa da kasa. A cewarsa, burin JKS shi ne kyautata zaman rayuwar al’umma da neman farfadowar kasar Sin baki daya. Inda take jagorantar al’ummomin Sin wajen neman ci gaba, wadda ta kuma sami amincewa da goyon bayan jama’ar kasar. Masanin ya ce, shirin “Ziri daya da hanya daya” da gwamnatin kasar ta fidda, ya karfafa mu’amalar dake tsakanin kasa da kasa, da kuma ba da gudummawa wajen kawar da talauci, yayin da ya inganta dunkulewar dukkanin bil Adama. Ko shakka babu, yadda JKS take dukufa wajen kula da jama’ar kasar ya zama abin koyi ga kasa da kasa. (Ahmad Fagam)