logo

HAUSA

Kafofin watsa labaru na kasashen yammacin duniya suna nuna bambanci ga aikin binciken sararin samaniya na kasar Sin

2021-05-17 16:50:08 CRI

Kafofin watsa labaru na kasashen yammacin duniya suna nuna bambanci ga aikin binciken sararin samaniya na kasar Sin_fororder_sararin samaniya-Bello_1

A ranar 15 ga watan Mayun da muke ciki, na’urar bincike mai taken “Tianwen-1” da kasar Sin ta harba ta sauka kan duniyar Mars, wannan batu ya sa ci gaban fasahar binciken sararin samaniya ta kasar Sin ya sake kama bangon farko na jaridun kasashe daban daban. Wasu kwanaki 18 da suka wuce, kasar Sin ta harba wani muhimmin bangare na tashar binciken sararin samaniya ta kasar. Kana a karshen shekarar 2020, nau’rar bincike mai taken “Chang’e-5” ta kasar Sin ta sauka kan duniyar wata.

Sai dai ganin saurin bunkasuwar harkar binciken sararin samaniya a kasar Sin ya sa wasu kafofin watsa labaru na kasashen yammacin duniya fara daukar wani ra’ayi na nuna bambanci. Kana wani bayanin da jaridar Financial Times ta kasar Birtaniya ta wallafa a kwanakin baya zai iya wakiltar wannan ra’ayi na kafofin watsa labarun kasashen yammacin duniya, inda wannan bayani mai taken “Burin kasar Sin: neman mutunci ko kuma kalubalantar kasar Amurka” ya ce, yunkurin raya aikin binciken sararin samaniya na kasar Sin zai haddasa gasa a tsakaninta da kasar Amurka a fannin karfin soja, saboda kasashen yammacin duniya ba su san dalilin da ya sa kasar Sin ke kokarin binciken sararin samaniya ba, shi ne domin samar da hidimomi ga jama’a, ko kuma domin neman raya fasahohin soja. Kana a cewar marubucin bayanin, rashin hadin gwiwa da sauran kasashe zai takaita alfanun da kasar Sin za ta samu ta hanyar raya fasahar binciken sararin samaniya.

Amma mene ne gaskiyar batun? Da farko dai, kasar Amurka ita kadai take gudanar da gasar karfin soja a duniya.

Kasar Sin ta taba gabatar da wata takardar bayani game da aikin binciken sararin samaniya na kasar a shekarar 2016, inda aka tabbatar da wata babbar ka’ida, wato” neman ci gaban fasahohi maimakon karuwar karfin soja”. Kana kasar Sin ta kan nanata ra’ayinta a wurare daban daban cewa “sararin samaniya na dukkan bil Adama ne, bai kamata a raya wasu makamai a sararin samaniya, ko kuma kaddamar da gasar karfin soja a can ba”. Hakika kasar Sin da kasar Rasha sun taba gabatar da shawara ga kasar Amurka har sau 2, don su yi shawarwari kan batun daddale yarjejeniyar magance gasar aikin soja a sararin samaniya. Sai dai kasar Amurka ta ki yarda. Saboda me? Saboda kasar Amurka na neman kafa rundunar musamman ta sararin samaniya.

Amurka ta fara kafa rundunar sararin samaniya a watan Yuni na shekarar 2018, bisa dalilin da shugaban kasar na lokacin Donald Trump ya bayyana kamar haka: “kasancewa a cikin sararin samaniya ba zai ishe kasar Amurka ba, tana bukatar wani matsayi na jagora”. Daga bisani kasar Amurka ta janye daga yarjejeniyar haramta amfani da makamai masu linzami na matsakaitan zango, tare da kafa hedkwatar sojojin sararin samaniya, da kaddamar da bincike kan wasu makaman da za a iya yin amfani da su a sararin samaniya. Sannu a hankali tana kokarin gabatar da wani tsarin daukar matakan soja a sararin samaniya.

Idan mun kwatanta ra’ayoyin Sin da Amurka dangane da sararin samaniya, za mu fahimci cewa, burin kasar Sin shi ne neman raya kimiyya da fasaha, yayin da kasar Amurka ke neman tabbatar da ikonta na fin karfi, da mulkin danniya. Saboda haka, abun da wasu kafofin watsa labaru na kasashen yammacin duniya suka bayyana, wai “ci gaban fasahohin kasar Sin ya sa ake samun gasar karfin soja tsakaninta da Amurka”, ba shi da gaskiya ko kadan. Za a iya hana kasar Sin samun ci gaban kimiyya da fasaha, don neman tabbatar da matsayin kasar Amurka na fin karfi a duniya? Ka ga ba zai yiwu ba.

Na biyu shi ne, kasar Sin har kullum tana son hadin gwiwa da sauran kasashe a fannin aikin binciken sararin samaniya.

Za mu iya daukar na’urar bincien duniyar Mars ta “Tianwen-1” a matsayin wani misali. Na tuna da cewa an nuna hotunan bidiyon harba na’urar “Tianwen-1” a watan Yulin bara, inda aka iya ganin tamburan hukumomin nazarin sararin samaniya na kungiyar EU, da na kasashen Faransa, da Argentina, da Austria, a kan babbar rokar da aka yi amfani da ita wajen harba na’urar “Tianwen-1”. Kana dalilin da ya sa haka, shi ne domin duk wadannan hukumomi sun shiga aikin tsarawa da harba na’urorin binciken. Ta wannan za mu iya ganin cewa, kasar Sin tana hadin gwiwa da sauran kasashe wajen gudanar da ayyukan binciken sararin samaniya, kana hadin gwiwar yana da zurfi.

Ban da wannan kuma, mihimmin bangaren tashar binciken sararin samaniya da kasar Sin ta harba a ranar 29 ga watan Afirlun bana, shi ma ya kunshi wasu ayyukan hadin kai guda 9, na wasu kasashe 17. Ko a cikin tashar binciken sararin samaniya da kasar Sin take kokarin ginawa ma an kebe wasu na’urori na musamman domin karbar bakuncin ‘yan sama jannati na sauran kasashe a nan gaba. Duk wadannan abubuwa shaidu ne da suka karyata zargin da kafofin watsa labaru na kasashen yammacin duniya suka yi wa kasar Sin, cewa wai “kasar Sin ba ta son hadin gwiwa da sauran kasashen a fannin aikin binciken sararin samaniya”.

Hakika kafofin watsa labarun kasashen yammacin duniya sun dade suna kokarin yada jita-jita game da aikin binciken sararin samaniya na kasar Sin. Misali, bayan da aka harba wani mihimmin bangare na tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin, wasu kafofin watsa labaru na kasashen yammacin duniya, maimakon mai da hankali kan ma’anar aikin game da fasahar binciken sararin samaniya ta duniya, sun yi kokarin yada jita-jita, cewa wai “tarkacen rokar kasar Sin zai fada wasu kasashen, tare da haddasa barna”. A lokacin wadannan kafofin watsa labaru, ciki har da CNN na kasar Amurka, sun yi kokarin rura wuta, har zuwa lokacin da tarkacen rokar ya fada cikin teku, kamar yadda kasar Sin ta yi hasashe.

Ainihin dalilin da ya sa ake yawan samun jita-jita da karairayi game da kasar Sin, a fannin aikin binciken sararin samaniya, shi ne domin kafofin watsa labaru na kasashen yammacin duniya ba su amince da yunkurin kasar Sin na raya aikin binciken sararin samaniya ba. Ba su yarda cewa, kasar Sin ta ware makudan kudi a fannin binciken sararin samaniya, don neman raya kimiyya da fasaha kadai ba.

Sai da wani abun da su kafofin watsa labaru ba su sani ba shi ne, bisa manufar da kasar Sin ta dauka ta raya kasa ta hanyar bunkasa kimiyya da fasaha, ta fi dora muhimmanci kan alfanun da za ta iya samu a nan gaba, inda take neman raya masana’antu ta wasu sabbin fasahohi, da yin amfani da ingantattun fasahohin da aka samu don amfanawa jama’a, da samar da kayayyakin da ake iya sayensu a kasuwa. Zuwa yanzu, fasahohi fiye da 2000 da kasar Sin ta samu ta hanyar raya fasahar binciken sararin samaniya, suna taimakawa raya tattalin arzikin kasar, kana bisa fasahar taurarin dan Adam, kasar na samun kudin da ya zarce Yuan biliyan 200 a duk shekara. A fannin harba kumbuna masu daukar mutane, duk kudin Sin Yuan 1 da kasar Sin ta zuba, za ta iya samun ribar da yawanta ya kai Yuan 10 zuwa 12.

Ban da wannan kuma, wani abu na daban da kafofin watsa labaru na kasashen yammacin duniya ba su fahimta ba, shi ne manufar kasar Sin ta kokarin kafa “Al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makoma ta bai daya”. Wannan manufa ta sa kasar Sin ke koakrin raya fasahohi masu alaka da sararin samaniya, don taimakawa dan Adam kara sanin duniyoyi daban daban, da habaka wuraren da mutane suke zama a ciki, da tabbatar da ci gaban al’adun dan Adam mai dorewa.

Dan saman jannatin kasar Amurka, Neil Armstrong, ya taba bayyana wata sahararriyar magana, yayin da ya hau duniyar wata a shekarar 1969, cewa “Takun da na yi a kan duniyar wata yau, babban ci gaba ne na daukacin dan Adam”. A lokacin, ana lura da darajar aikin binciken sararin samaniya ga dan Adam. Sai dai, zuwa yanzu, kafofin watsa labarai na kasashen yammacin duniya sun riga sun manta da darajar. (Bello Wang)

Bello