logo

HAUSA

Sin ta kasance babbar mai cin moriya kuma babbar mai ba da gudummawa ga tsarin cinikayya tsakanin kasashe da dama

2021-05-17 13:40:57 cri

Tsohon Mataimakin Darakta-Janar WTO: Sin ta kasance babbar mai cin moriya kuma babbar mai ba da gudummawa ga tsarin cinikayya tsakanin kasashe da dama bayan shigar ta cikin kungiyar_fororder_695

A bana kasar Sin ke cika shekaru 20 da shiga kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO a takaice. Yi Xiaozhun, tsohon Mataimakin Darakta-Janar na kungiyar WTO, wanda ya sauka daga mukaminsa ba da dadewa ba, ya bayyana a wajen wani taron kara wa juna sani a kwanakin baya cewa, a cikin shekarun nan 20 da kasar Sin ta yi cikin kungiyar, ta kasance babbar kasar da ke cin gajiyar tsarin cinikayya tsakanin kasashe da dama, kuma ita ce babbar mai ba da gudummawa ga kungiyar ta WTO. Ya yi imanin cewa, ya kamata kasar Sin ta taka rawar da ta dace da amfani da matsayinta wajen yi wa kungiyar kwaskwarima.

A yayin taron kara wa juna sani mai taken "Makomar yi wa kungiyar WTO kwaskwarima da matsayin da kasar Sin ke dauka" wanda kungiyar kwararru ta CCG ta gudanar a 'yan kwanakin da suka gabata, Yi Xiaozhun, tsohon mataimakin darekta janar na kungiyar WTO kuma tsohon mataimakin ministan kasuwanci na kasar Sin, ya bayyana cewa, a cikin shekaru 20 da kasar Sin ta yi a WTO, baya ga kasancewarta wadda ta fi cin gajiyar tsarin cinikayya tsakanin kasashe da dama, ta kasance babbar mai ba da gudummawa ga tsarin cinikayya tsakanin kasashe da dama. Ya ambato alkaluma daga kungiyar WTO yana cewa:

“A cikin shekaru 20 da suka gabata, jimillar cinikin kayayyakin duniya ya kusan ninkawa sau daya, amma yawan kayayyakin da kasar Sin ta fitar ya karu da sama da sau 7. A lokaci guda kuma, jimillar kayayyakin da kasar Sin ke shigowa da su ta karu da kusan sau 6. Wannan sau 6, hakika lamba ce mai matukar mahimmanci, wadda ita ce gudummawar da muka bayar ga duniya. Kayayyakin da kasar Sin ta shigo da su a shekarar da ta gabata, sun kai kashi 12% bisa yawan kayayyakin da kasashe suka shigar a duk duniya. A gani na, wannan adadi ne mai ban mamaki.”

Tsohon Mataimakin Darakta-Janar WTO: Sin ta kasance babbar mai cin moriya kuma babbar mai ba da gudummawa ga tsarin cinikayya tsakanin kasashe da dama bayan shigar ta cikin kungiyar_fororder_718

Shigar kasar Sin cikin kungiyar WTO, ya sauya tsarin cinikayya na kasashe daban-daban na duniya, wanda ke da amfani ga jama’a a duk duniya, musamman ma kasashe masu tasowa. Dangane da gudanar da kasuwanci tare da kasashe masu tasowa, Yi Xiaozhun ya ba da misali cewa:

“Kasar Sin ta kasance daya daga cikin muhimman kasashe masu tasowa kalilan a cikin kungiyar WTO wadanda suka yi alkawarin soke karbar harajin kwastan kan kaso 97% na kayayyakin cinikayya da kasashe mafiya rashin ci gaba suka fitar. Tun daga shekara ta 2008, kasar Sin ita ce babbar kasar da kasashe mafiya rashin ci gaba suka shigar da kayayyakinsu, ta kuma karbi kashi 1 cikin kashi 4 na baki dayan kayayyakin da kasashe mafiya rashin ci gaba ke fitarwa.”

Yi Xiaozhun ya nuna cewa, a daya hannun, ya kamata kasar Sin ta amince da rawar da take takawa a kungiyar WTO, a daya hannun kuma kada ta yi sakaci. A ganinsa, ba za a dakatar da bude kofa ga kasashen waje da yin kwaskwarima a cikin gidan kasar Sin ba. Ya kuma nuna cewa, yayin da ake aiwatar da garambawul a kungiyar WTO, ya kamata kasar Sin ta taka rawa ta musamman. 

“Ta yaya kasar Sin za ta iya amfani da matsayinta a cikin kungiyar WTO yadda ya kamata, wajen inganta tsarin cinikayya tsakanin kasashe da dama bisa hanyar gudanar da cinikayya cikin ‘yanci da sauki, maimakon komawa hanyar ba da kariyar cinikayya? Ina tsammanin wannan sabon batu ne dake gaban gwamnati, da kamfanoni da bangaren ilmi na kasar ta Sin.” (Bilkisu)