logo

HAUSA

Masu zuba jari na son yin kasuwanci a Cape Town duk da annobar COVID-19

2021-05-14 11:44:24 CRI

Masu zuba jari na son yin kasuwanci a Cape Town duk da annobar COVID-19_fororder_南非

Birnin Cape Town na kasar Afrika ta kudu ya sanar cewa, masu zuba jari na cikin gida da ketare suna da kwarin gwiwar ci gaba da hada hadar kasuwanci a birnin, inda suka buga misali game da bunkasuwar ayyukan samar da kayayyakin more rayuwa da tsara gine-gine wadanda aka amince da su sama da shekara guda da ta gabata.

A sanarwar da magajin birnin Dan Plato ya fitar ya ce, ingantaccen yanayin zuba jari mai dorewa a birnin Cape Town zai kara tabbatar da samun dawwamamman yanayin zuba jari na dogon lokaci a birnin, kana zai bunkasa damammakin samar da guraben ayyukan yi ga mazauna wurin.

Bunkasa ayyukan samar da kayayyakin more rayuwa da tsara gine-gine wanda ya kai na kudin kasar rand biliyan 14 kwatankwacin dala miliyan 993, ya kasance a matsayin wani babban aiki mai matukar girma a tsakiyar birnin kasuwancin, zai samar da guraben aikin yi kusan 13,000 a lokacin gudanar da ayyukan gine-ginen, da sauran wani aiki mai zaman kansa shi ma zai samar da guraben aiki kusan 5,200, sannan ayyukan kai tsaye na gine-ginen za su samar da guraben aiki 19,000 na kai tsaye.

Tsakanin watan Maris na shekarar 2020 da watan Afrilun 2021, birnin ya amince da ayyukan gine-gine guda 18,070 wanda ya kai ran kusan biliyan 17.2, a makon jiya an sanar da wani aikin fadada wasu wurare da ya kai ran biliyan 3.9 a yankin Victoria da Alfred Waterfront, waje mafi shahara a duniya dake daukar hankalin masu yawon bude ido.(Ahmad)