logo

HAUSA

Me ya sa kasar Sin take saurin jawo jarin waje?

2021-05-14 21:18:47 CRI

Me ya sa kasar Sin take saurin jawo jarin waje?_fororder_A

Kamfanin dillancin labarai na RIA Novosti na kasar Rasha, ya wallafa wani bayani a kwanan nan, inda a ciki aka nuna cewa, kasar Sin tana kara saurin jawo jarin waje, wanda ba’a taba ganin irinsa ba a tarihi.

Bisa sabbin alkaluman da ma’aikatar kasuwancin kasar ta bayar jiya Alhamis, daga watan Janairu zuwa Afrilun bana, an kafa kamfanoni 14,533 a kasar Sin, wadanda kasashen waje suka zuba jari a cikin su, adadin da ya karu da kaso 50.2 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokaci a bara. Kana, yawan jarin wajen da kasar Sin ta yi amfani da shi a zahiri, ya kai Yuan biliyan 397.07, adadin da ya karu da kaso 38.6 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara.

Shin ko ina dalilin da ya sa jarin waje ke ta shigowa kasar Sin? Babban dalilin da ya sa haka shi ne, kasar Sin tana da cikakkun masana’antu, da kwarewar yin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha, da ingantaccen tsarin sufurin kaya, tare kuma da tagomashin al’umma. Duk wadannan abubuwa za su taimaka sosai, ga rage yawan kudaden da kamfanoni masu jarin waje suke kashewa, kana za su sanya sabon kuzari ga ci gaban tattalin arziki.

Me ya sa kasar Sin take saurin jawo jarin waje?_fororder_B

Har wa yau, babbar kasuwar dake da yawan al’umma fiye da biliyan 1.4, na zama muhimmin jigon habakar tattalin arzikin kasar Sin. Ko a shekara ta 2020, wadda annobar COVID-19 ta fi yi wa illa, bisa binciken da ma’aikatar kasuwancin kasar ta yi, akwai kusan kaso 60 bisa dari na kamfanoni masu jarin waje dake kasar Sin, wadanda suka samu karuwar moriya.

A ‘yan shekarun nan, gwamnatin kasar Sin tana kara bude kofar ta ga kasashen waje, da kyautata dokokin da suka shafi jarin waje, a wani kokari na kirkiro yanayi mai kyau ga kamfanonin kasashen ketare.

Har yanzu akwai rashin sanin tabbas game da annobar COVID-19, gami da makomar farfadowar tattalin arzikin duniya, kuma kasar Sin tana fuskantar kalubale a bangaren jawo jarin waje. Amma duk da haka, nasarorin da kasar ke samu, na sanya kalaman da suka shafi raba kawuna da kasar Sin, da wasu sassa ke kokarin yayatawa, zama tamkar abun dariya. (Murtala Zhang)