logo

HAUSA

Africa CDC: Kasashen Afirka sun samu sama da alluran riga kafin COVID-19 miliyan 38

2021-05-14 10:22:20 CRI

Africa CDC: Kasashen Afirka sun samu sama da alluran riga kafin COVID-19 miliyan 38_fororder_210513-Africa CDC

Cibiyar kandagarki da dakile yaduwar cututtuka ta Afirka (Africa CDC), ta sanar a jiya Alhamis cewa ya zuwa yanzu, kasashen nahiyar sun samu sama da alluran riga kafin annobar COVID-19 miliyan 38.03.

Africa CDC, kwararriyar hukumar kiwon lafiya ta kungiyar tarayyar Afirka mai mambobi kasashe 55, ta bayyana cewa ya zuwa yanzu, kasashen kungiyar sun yiwa mutane riga kafi miliyan 22.4 daga cikin sama da allurai miliyan 38.03 da suka karba.

A cewar cibiyar, wannan adadi ya yi daidai da kaso 1.48 na yawan mutanen da aka yiwa rigakafi a nahiyar, abin da ke nuna cewa, kaso 0.40 na yawan al’umma nahiyar sun karbi cikakken riga kafin da ake bukata.

Cibiyar ta kara da cewa, kasashen nahiyar sun yi amfani da kusan kaso 58.87 na alluran da suka karba ya zuwa wannan lokaci.

Kasashen Morocco, da Najeriya da Habasha da Masar da Kenya ne suke kan gaba, wajen yiwa al’ummominsu riga kafin annobar. (Ibrahim)