An gano ragowar wani tsohon birni mai tarihin sama da shekaru 3000 da suka gabata a Luxor
2021-05-14 20:36:43 cri
An gano ragowar wani tsohon birni mai tarihin sama da shekaru 3000 da suka gabata a Luxor, wani gari a kudancin Masar. A cewar rahotanni, an gina wannan tsohon gari a zamanin Amenhotep III, kuma masu binciken kayan tarihi sun ce shi ne "birni" mafi girma da aka samu a kasar. (Bilkisu)