logo

HAUSA

Yunkurin nuna adawa da kasar Sin da wasu kasashe kalilan ke yi ko kadan bai yi tasiri a MDD ba

2021-05-13 21:55:41 CRI

Yunkurin nuna adawa da kasar Sin da wasu kasashe kalilan ke yi ko kadan bai yi tasiri a MDD ba_fororder_微信图片_20210513211323

Har yanzu dai wasu tsirarun kasashen yammacin duniya ciki har da Amurka, suna ta yunkurin nuna adawa da kasar Sin. Jiya Laraba, Amurka da Birtaniya da Jamus, gami da wasu kungiyoyin da ba na gwamnati ba, sun kira wani taro da suka ce wai na gefe ne kan yanayin hakkin dan Adam a jihar Xinjiang ta kasar Sin.

Taron dake cike da makircin siyasar wasu kasashe na adawa da kasar Sin, ya shaida ainihin makasudin su, wato amfani da batun da ya shafi Xinjiang don hana ci gaban kasar Sin. Wasu kasashen yammacin duniya kalilan sun yi haka ne da nufin cimma muradunsu na siyasa.

Sanin kowa ne, batun jihar Xinjiang, batu ne da ya shafi yaki da ta’addanci, tare kuma da kawar da masu tsattsauran ra’ayi, don haka sam ba batu ne da ya shafi hakkin dan Adam ba.

Yunkurin nuna adawa da kasar Sin da wasu kasashe kalilan ke yi ko kadan bai yi tasiri a MDD ba_fororder_微信图片_20210513211328

A halin yanzu, ana kara samun kasashen da suke fahimtar ainihin halin da ake ciki dangane da jihar Xinjiang. Alal misali, akwai kafafen yada labarai da dama na kasashen Australiya, da Brazil, da Singapore gami da Sweden, wadanda suka wallafa bayanai kwanan nan, inda suka jinjinawa kasar Sin, saboda nasarorin da ta cimma a fannin yaki da ta’addanci a Xinjiang, da bankado makarkashiyar siyasar da kasashen yamma suke kullawa. Har ma wasu kafofin watsa labaran Sweden da Amurka, sun wallafa bayani, ko kuma bullo da rahoton dake cewa, babu shaidun dake nuna cewa wai ana tilasta aiki, ko aikata kisan kare-dangi a jihar ta Xinjiang.

Alal hakika, duk wani yunkuri da Amurka ke yi na jirkita gaskiya, tare da sauran wasu tsirarun kasashe, wannan yunkurin nasu game da jihar Xinjiang ya riga ya sha kaye a MDD. Kuma idan sun ci gaba da yin hakan, za su rasa kimar su.(Murtala Zhang)