Rahoton kidayar al’ummar kasar Sin ya karyata furucin kasashen yammaci
2021-05-13 18:46:46 CRI
Kafin kasar Sin ta gabatar da alkaluman kidayar al’ummarta a kwanan baya, jaridar “Financial Times” ta Birtaniya a wani rahotonta ta ruwaito wata majiya dake cewa, karon farko yawan al’ummar Sin ya ragu. Amma, alkaluman kidayar al’umma da Sin ta fitar a ran 11 ga wata na nuna cewa, yawan al’ummar Sin ya kai biliyan 1 da miliyan 411 da dubu 780, adadin da ya karu sannu hankali a cikin shekaru 10 da suka gabata, karuwar da ta kai kaso 0.53 a kowa ce shekara.
Sai dai wannan ya sa wasu kafofin yada labarai na kasashen yamma suka mai da martani da sauri, suna mai cewa saurin karuwar yawan al’ umma a kasar Sin a wannan karo ya ragu sosai tun daga shekaru 60 da suka gabata. Ita ma jaridar “The New York Times”ta wallafa wani bayanin da kan labari ke zama mai girgiza mutane yana mai cewa, yawan jariran da aka haifa ya ragu, kuma yawan tsoffi na karuwa, abin dake kawo barazanar tattalin arziki ga jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin da al’ummarta, abin da ya nuna cewa, Sin tana fuskantar matsalar yawan mutane mai tsanani. Wannan bayani ya ruwaito kalaman wani masani na cewa, ana iya yin hasashen cewa, Sin ba za ta zarce Amurka ba a fannin tattalin arziki saboda ganin wannan matsala.
To, shin ko wadannan kafofin yada labarai sun fadi hakikanin hali da ake ciki a wannan fanni a Sin? Bari mu kalli alkaluman da aka fitar.
Alkaluman kididdiga na nuna cewa, yawan al’umma masu shekaru tsakanin 0 zuwa 14 ya karu da kashi 1.35% a cikin shekaru 10 da suka gabata, wanda ya kai kashi 17.95 na dukkan al’ummar kasar. Matakin da ya nuna cewa, yawan al’umma na karuwa inda kuma yawan jarirai da kananan yara ke karuwa a lokaci daya, wannan alama na bayyana cewa, duk da raguwar yawan haihuwar jarirai bisa na dukkan al’umma, amma yawan al’umma yana karuwa, matakin da zai samar da isassun ‘yan kwadago nan gaba, kuma kwalliya ta biya kudin sabulu, kasar Sin ta cimma nasara bisa ga yadda ta daidaita manufarta ta fuskar haihuwa. A hakika dai, raguwar jariran da ake haihu, matsala ce da yawancin kasashe masu ci gaba suke fuskanta yanzu, kila Sin za ta fuskanci wannan kalubale nan gaba.
Kazalika, kididdigar na nuna cewa, yawan al’umma masu shekaru tsakanin 16 zuwa 59 ya kai miliyan 880, kuma matsakaicin shekarun al’ummar Sin ya kai 38.8, wannan adadi ya nuna cewa, yawan masu jini a jika a kasar ya kai fiye da kashi 60%, wadanda suke taka muhimmyar rawa wajen raya kasar Sin. Ban da wannan kuma, yawan al’ummar Sin da suka samu ilmi na zamani sun karu matuka. Bayanai na nuna cewa, yawan mutane da suka kammala karatun digiri na farko a kasar ya kai 15467 daga cikin ko wadanne mutane dubu 100 a shekarar 2020, kwatankwacin 8930 daga cikin ko wadanne dubu 100 kawai a shekarar 2010, yawan shekaru da mutane masu shekaru fiye da 15 suka kwashe wajen samun ilmi ya karu zuwa 9.91 a shekarar 2020 daga 9.08 a shekarar 2010.
Amma, a hakika Sin tana fuskantar matsalar karuwar tsoffi, yawan tsoffi ya kai 18.7%, wanda ya karu da kashi 5.44%, abin lura shi ne, daga cikinsu, wadanda suka kammala karatun sakandare ko fiye da haka sun kai miliyan 36.69, adadin da ya karu da miliyan 20.85 bisa na shekarar 2010, wato ke nan suna iya ci gaba da ba da gudummawarsu a bunkasuwar tattalin arziki da al’ummar Sin. A wani bangare kuma, karuwar tsoffi wata matsala ce da duk duniya ke fuskanta, kasar Sin ba kasa daya kadai ke fuskantar wannan matsala a duniya ba, kuma ana iya ganin zarafi da ya kawo mana, wato karuwar tsoffi na nuna cewa, yawan tsawon shekarun Bil Adama na karuwa, don haka, akwai bukatar baiwa tsoffi kulawa ta jiyya da hidimma yadda ya kamata
Yawan al’ummar Sin na karuwa, kuma suna kara samun ilmi mai inganci. Rahoton kidayar al’ummar kasar Sin ya nuna cewa, karairayin da wasu kasashen yamma suke yayata game da matsalar yawan al’ummar Sin ba su da gaskiya. (Amina Xu)