logo

HAUSA

Kasar Sin ba ta da burin boye alluran rigakafin COVID-19

2021-05-12 16:58:50 CRI

Kasar Sin ba ta da burin boye alluran rigakafin COVID-19_fororder_微信图片_20210512161453

Tun lokacin da annobar COVID-19 ta barke a shekarar 2019, kasashen duniya da kamfanonin harhada maguguna suka shiga aikin binciken samar da alluran riga kafin wannan annoba da ke ci gaba da addabar wasu sassan duniya.

Sai dai tun bayan da aka yi nasarar samun irin wadannan alluran rigakafi, wasu kasashe da ma irin wadannan kamfanoni, suke boye wa ko kokarin mallakar alluran rigakafi don amfanini al’ummominsu ko kokarin siyasantar da batun, don biyan bukatunsu na siyasa maimakon ceton rayukan al’umma. Sabanin irin wadannan kasashe na yammacin duniya da ’yan korensu, kasar Sin tun farko ta yi allkawarin cewa, idan har ta yi nasarar gudanar da bincike ta kuma yi nasarar samar da alluran riga kafin cutar COVID-19, to, duniya baki daya za ta ci gajiyarsa, musamman kasashe masu tasowa.

Kuma duk mai bibiyar al’amura, ya tabbatar da cewa, kasar Sin ta cika wannan alkawari, su ma kamfanonin kasar ta Sin dake aikin samar da riga kafin, sun sauke nauyin dake bisa wuyansu, inda suka kulla yarjejeniyar samar da alluran riga kafin tare da wasu kasashe, a kokarin ganin an yaki wannan annoba cikin hadin gwiwa. Misali na baya-bayan nan, shi ne yadda kasar Masar za ta rika samar da alluran COVID-19 na kamfanin Sinovac a cikin gidanta, tare da kamfanin nazarin sarrafa kwayoyin halittu na Masar (VACSERA), inda za a rika kiran alluran da sunan Sinovac-Vacsera.

Yanzu haka kuma, hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta amince da amfani da riga kafin kasar Sin na kamfanin Sinopharm cikin alluran riga kafin da WHO ta amince da su wajen yin amfanin gaggawa. Wannan mataki, ya sanya alluran riga kafin na Sinopharm na kasar Sin, zama daya tilo da ba na kasashen yamma ba, abin da masana ke cewa, wani kyakkyawan albishir ne da zai taimakawa kasashen dake matukar bukatar miliyoyin rigakafi a duniya. Don haka, galibin kasashe masu tasowa suna da zabi mai sauki na samun rigakafin.

Yanzu haka dai, ana amfani da alluran rigakafin kasar Sin a kasashe da dama na duniya, abin dake nuna ingancin rigakafin na Sin da ma yadda kasar Sin ke sauke nauyin dake bisa wuyanta a fannin samar da rigakafi, da ma yaki da wannan annoba a duniya ba kuma tare da gindaya wani sharadi na siyasa ba.

Wannan labari ya sa kasar Zambia ta yanke shawarar sanya alluran riga kafin Sinopharm na kasar Sin, cikin shirinta na riga kafi na kasa. Baya ga batun riga kafin COVID-19, da taimakon da kasar Sin take samarwa kasashe a fannoni daban-daban game da yaki da wannan annoba, wata tawagar ma’aikatan lafiyar kasar Sin ta isa lardunan arewacin kasar Laos bisa bukatar kasar, don taimaka mata yaki da wannan annoba, da kuma yadda za ta koyawa takwarorinta na kasar ta Laos dabarun yaki da annobar COVID-19.

Ita ma kungiyar Red Cross ta kasar Sin ta bi sahun gwamnati da kamfanonin kasar Sin, wajen agazawa kasar Indiya da tsabar kudi har dala miliyan 1, domin yaki da annobar COVID-19. Haka kuma kungiyar ta samar mata da kayayyakin kiwon lafiya da suka hada da iskar shaka ta Oxygen, da na’urar taimakawa numfashi da kyallen rufe baki da hanci, da magunguna da sauran muhimman kayayyakin kiwon lafiya da ake bukata. Wannan mataki na kasar Sin, shi ake nufi da ma’anar hadin gwiwar bangarori da gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adama, ta yadda za a gudu tare a tsira tare. (Ibrahim Yaya)