An yi harbi a wata makaranta dake birnin Kazan na kasar Rasha
2021-05-12 09:41:27 CRI
Bisa labarin da aka bayar, an yi harbi a wata makaranta dake birnin Kazan na kasar Rasha. Ya zuwa yanzu, lamarin ya haddasa mutuwar mutane 8 tare da raunata mutane kimanin 20. A halin yanzu, an shiga yanayin yaki da ta'addanci a birnin, da daukar matakan kiyaye tsaro a dukkan cibiyoyin bada ilmi na birnin.