logo

HAUSA

Somaliya ba ta ji dadin matakin Kenya na haramta jiragen sama shiga kasarta ba

2021-05-12 10:50:50 CRI

Somaliya ba ta ji dadin matakin Kenya na haramta jiragen sama shiga kasarta ba_fororder_210512-Somalia Air

Gwamnatin kasar Somaliya ta ce, ba ta ji dadin shawarar da kasar Kenya ta yanke ta dakatar da jiragen saman fasinja daga zuwa da kuma wadanda suka fito daga Mogadishu, babban birnin kasar ba.

Ministan sufuri da zirga-zirgar jiragen sama na kasar Somaliya Duran Farah, ya bayyana cewa, shawarar da kasar Kenya ta yanke, zai gurgunta dangantakar diflomasiya da makwabtan kasashen biyu da ba a taba da dawo da ita ba.

A cewar hukumar kula da zirga-zirgar jiragen saman Kenya (KCAA), jiragen sama dake jigilar kayayyakin lafiya da na jin kai ne kadai za a bari su shiga kasar.

Matakin Kenya na zuwa ne, kwana guda bayan da Somaliya ta sanar a ranar Lahadin da ta gabata cewa, za ta ci gaba da haramta shigo da Khat, wani maganin gargajiya dake kara kuzari daga Kenya, duk da dawo da huldar diflomasiya tsakanin kasashen biyu.

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasar Somaliya (SCAA) ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa, matakin gwamnati na haramta shigo da maganin gargajiya dake kara kuzari, yana nan daram. (Ibrahim)