Yadda Sin take hadin gwiwa da kasashen duniya kan yaki COVID-19
2021-05-12 08:55:29 CRI
Lokacin da annobar COVID-19 ta barke a shekarar 2019, ba zato ba tsammani, kasashen duniya da kamfanonin harhada maguguna suka shiga aikin binciken samar da alluran riga kafin wannan annoba da ke ci gaba da addabar wasu sassan duniya.
Sai dai tun bayan da aka yi nasarar samun irin wadannan alluran riga, wasu kasashe da irin wadannan kamfanoni, suke boye wa ko kokarin mallakar alluran riga don amfanini al’ummominsu ko kokarin siyasantar da batun, don biyan bukatunsu na siyasa maimakon ceton rayukan al’umma. Sabanin irin wadannan kasashe na yammacin duniya, kasar Sin tun farko ta yi allkawarin cewa, idan har ta yi nasarar gudanar da bincike ta kuma yi nasarar samar da alluran riga kafin cutar COVID-19, duniya za ta ci gajiyarsa, musamman kasashe masu tasowa. Kuma ta cika wannan alkawari.
Su ma kamfanonin kasar ta Sin dake aikin samar da riga kafin, sun kulla yarjejeniya samar da alluran riga kafin tare da wasu kasashe, a kokarin ganin an yaki wannan annoba cikin hadin gwiwa. Na baya-bayan nan, shi ne yadda kasar Masar za ta rika samar da alluran COVID-19 na kamfanin Sinopharm a cikin gidanta, tare da kamfanin nazarin sarrafa kwayoyin halittu na Masar (VACSERA), inda za a rika kiran alluran da sunan Sinovac-Vacsera.
Ita ma hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta amince da amfani da riga kafin kasar Sin na kamfanin Sinopharm cikin alluran riga kafin da WHO ta amince da su wajen yin amfanin gaggawa, saboda inganci da tsaronsa.
Wannan mataki, ya sanya alluran riga kafin na Sinopharm na kasar Sin, za ma daya tilo da ba na kasashen yamma ba, abin da masana ke cewa, wani kyakkyawan albishir ne da zai taimakawa kasashen dake matukar bukatar miliyoyin riga kafi a duniya.
Wannan labari, ya sa kasar Zambia yanke shawarar sanya alluran riga kafin Sinopharm na kasar Sin, cikin shirinta na riga kafi na kasa. Baya ga batun riga kafin COVID-19, da taimakon da kasar Sin ta ke samarwa kasashe a fannoni daban-daban game da yaki da wannan annoba, wata tawagar ma’aikatan lafiyar kasar Sin ta isa lardunan arewacin kasar Laos bisa bukatar kasar, don taimaka mata yaki da wannan annoba, da kuma yadda za ta koyawa takwarorinta na kasar ta Laos dabarun yaki da annobar COVID-19.
Ita ma kungiyar Red Cross ta kasar Sin, ta bi sahun gwamnati da kamfanonin kasar Sin, wajen agazawa kasar Indiya da tsabar kudi har dala miliyan 1, domin yaki da annobar COVID-19. Haka kuma kungiyar ta samar mata da kayayyakin kiwon lafiya da suka hada da iskar shaka ta Oxygen, da na’urar taimakawa numfashi da kyallen rufe baki da hanci, da magunguna da sauran muhimman kayayyakin kiwon lafiya. Da fatan za a guda tare a tsira tare. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)