logo

HAUSA

Wannan babbar kasuwar sayayya ta samar da dama ta cin gajiya ga duk duniya

2021-05-11 20:40:04 cri

Wannan babbar kasuwar sayayya ta samar da dama ta cin gajiya ga duk duniya_fororder_微信图片_20210511203845

An rufe bikin baje kolin sayayya na kasa da kasa na farko na kasar Sin a jiya Litinin a lardin Hainan, kasar Sin. A cikin kwanaki 4, kamfanoni 1,505, da samfurori dubu 2,628 daga kasashe da yankuna 70 sun halarci baje kolin, wanda kuma ya samu halarar mutane dubu 240. Baje kolin ya zama gaggarumin bikin sayayya na duk duniya.

Kididdigar da aka yi ta nuna cewa, daga cikin nau'ikan 2628 da suka halarci bikin bajen kolin, samfurorin kasashen waje sun kai kaso 51.9%. Ana iya cewa, karuwar karfin sayayya na Sinawa na kara samar da moriya ga kamfanonin sayayya na duniya.

Wannan babbar kasuwar sayayya ta samar da dama ta cin gajiya ga duk duniya_fororder_微信图片_20210511203904

Abun da ya fi mahimmanci shi ne, yanzu kasar Sin tana kokarin inganta bude kofa ga kasashen waje, don kara kafa makomar sayayya mai kyau a nan gaba. A hakika dai, lardin Hainan, inda aka gudanar da baje kolin, tashar jiragen ruwa ta cinikayya cikin ‘yanci ce da kasar Sin ke kokarin ginawa, bisa ma’aunin kasa da kasa.

A ranar da aka rufe bikin baje kolin, kamfanonin cikin gida da na waje guda 42, ciki har da L'Oréal, Parker, Deloitte, da sauransu, sun jagoranci sanya hannu kan yarjejeniya, kuma sun yi niyyar ci gaba da halartar baje kolin na biyu.

Ko shakka babu, wannan babbar kasuwar da ke kunshe da yawan al’umma fiye da biliyan 1.4, ta kasance dama da duniya baki daya ke iya cin gajiyarta. (Mai fassara: Bilkisu)