logo

HAUSA

Ya kamata kasashen duniya su yi tir da matakan Amurka da kawayenta na ci gaba da kutse cikin harkokin gidan Sin

2021-05-11 17:19:11 CRI

Ya kamata kasashen duniya su yi tir da matakan Amurka da kawayenta na ci gaba da kutse cikin harkokin gidan Sin_fororder_微信图片_20210511171005

Ofishin tawagar kasar Sin dake Majalisar Dinkin Duniya, ya bayyana rashin gamsuwar kasar da daukacin al’ummarta, tare da adawa mai karfi ga wani taro na gefe da Amurka da Birtaniya da Jamus da wasu tsirarun kungiyoyi masu zaman kansu, ke shirin gudanarwa dangane da abun da suke kira da yanayin hakkin dan Adam a jihar Xinjiang ta kasar Sin.

Amurka da kawayenta sun yi nisa ba sa jin kira, a yunkurinsu na ci gaba da ganin sun takaita ko dakile ci gaban kasar Sin tare da haifar da hargitse a kasar dake more zaman lafiya. Yayin da ake kiraye-kirayen hada hannu wajen yaki da ta’addanci da wanzar da zaman lafiya a duniya, da alama ba haka zancen yake ba a wajen Amurka da kawayenta, domin dukkan alamu sun nuna cewa, zaman lafiyar dake akwai a kasar Sin suke son hargitsawa ta kowanne hali.

Ko a kwanakin baya, kwamitin harkokin wajen majalisar wakilan Amurka, ya kira wani taro wai na sauraron ra’ayi kan batun yankin Xinjiang na kasar Sin. Kuma an lura cewa, mahalarta taron sun hada da masu neman ballewar jihar Xinjiang da masu adawa da manufofin da kasar Sin take aiwatarwa a yankin. Idan har Amurka da kawayenta da gaske batun kare hakkin dan Adam suke yi, to kamata ya yi a saurari ra’ayin al’ummar Sinawa da su kansu al’ummar Xinjiang, domin sanin ainihin yanayin da yankin ke ciki.

Kwararan shaidu sun tabbatar da ci gaban Xinjiang. A cikin shekaru sama da hudu da suka gabata, babu wani harin ta’addanci da aka kai yankin ko da sau daya, wanda ke da alaka da kokarin da gwamnatin kasar Sin take yi. Baya ga haka, an samu ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’umma a yankin yadda ya kamata, inda matsaikacin karuwar alkaluman GDP a kowace shekara tsakanin shekarar 2014 zuwa ta 2019 ta kai kaso 7.2 cikin dari.

A baya-bayan nan ne kuma wasu masharhanta uku, ciki har da tsohon magajin garin Norway suka bankado mutanen da suka tsara rahoton da ake cewa mai zaman kansa ne wanda aka yi wa lakabi da “Kisan Kiyashin Uygur”. Masharhantan sun ce sun bibiyi cibiyoyi biyu na The Newlines da The Raoul Wallenberg da suka rubuta wancan rahoto, kuma sun gano cewa suna da wata boyayyar manufa, haka kuma cibiyoyin ba su da inganci, domin ko a shekarar 2019 hukumar tantance cibiyoyin ilimi ta Virginia, ta kusa karbe lasisin cibiyar The New Lines.

Wannan kadai shaida ce dake nuna cewa, Amurka na fakewa ne kawai da batun hakkin dan adam, amma a hakika, ba hakan take nufi ba. Kamar yadda ofishin na kasar Sin ya bayyana, hakar Amurka da kawayenta ba za ta taba cimma ruwa ba, kuma ya kamata kasashen duniya su yi watsi tare da yin tir da irin karairayin da suke shirgawa. (Faeza Mustapha)