Isra’ila ta kai hari da makaman roka kan yankin Zirin Gaza
2021-05-11 10:15:40 CRI
Rahotanni daga bangarorin Isra’ila da Palasdinawa na cewa, bangaren Isra’ila ya yi ruwan rokoki kan yankin zirin Gaza har zuwa daren Litinin, inda ya yi sanadin mutuwar a kalla mutane 20.
Bayan jikkatar daruruwan Palasdinawa sakamakon arangama da ’yan sandan Isar’ila a gabashin brinin Kudus a ranar Litinin da safe, ita ma kungiyar Hamas ta kaddamar da harin roka kan yankin birnin Kudus da yammacin wannan rana, abin da ya sa Isra’ila mayar da martani mai muni.
Mai magana da yawun rundunar sojan Isra’ila, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, jiragen yakin Isra’ila sun kai hari kan wani ramin karkashin kasa da mayakan Hamas ke amfani da shi. Kafofin watsa labaran Isra’ila na cewa, yayin wannan hari, an kashe ’yan bindiga da dama a ramin karkashin kasar.
Bugu da kari, sojojin saman Isra’ila sun kara kai hari kan wuraren Hamas, ciki har da makaman harba rokoki guda biyu da tashohin sojoji guda biyu.
Ma’aikatar lafiya da kungiyar Hamas ke kula da ita a zirin Gaza, ta bayyana cikin wata sanarwa cewa, an kashe mutane 20, ciki har da yara 9, kana wasu 65 sun jikkata sanadiyar wata fashewa da ta faru ranar Litinin da yamma a garin Beit-Hanoun dake arewacin zirin Gaza. (Ibrahim)